entertainmentTrending

An Cafke Kwararren Mai Askin Batanci A Sabon Gari Dake Jahar Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani wanzami daga jihar Benuwe, Elijah Ode, bisa zargin sa Da Yiwa Mutane Askin Batanci A Jahar Kano wanda hakan ya sabawa addinin Musulunci.

 

Shidai Wannan Mai Askin Wanda Dan Asalin Jahar Benue Ne Yana Zaune A Yankin Sabongari da ke jihar Kano.

An samu labarin cewa rundunar ‘yan Hisbah ta Jahar Kano Ce ta bayar da rahoton gurfanar da Ode a ranar Talata.

Mai Askin Batanci A Kano

sannan kuma suka tura shi Izuwa Kotu Don A Yanke Masa Hukunci. A cewar wani mai fafutukar Kare Hakkin Dan Adam a jihar Benuwe, Mai Suna Smith Akoko, wanda Shine ya fara bayyana wa ‘yan Najeriya batun a kafafen Sadarwa Da Nufin Akaiwa Mai Askin Taimako Dan A Kubutar Dashi Daga Fuskantar Hukuncin Abinda Ya Aikata,

wanzamin, wanda shi ma dalibi ne, an kama shi a ranar Larabar da ta gabata, bayan an kama wasu Dauke Da Wannan Askin Batancin Akan su da ake ganin ya saba wa addinin Musulunci. .

Dan uwan ​​nasa, Sunday Ukenya, wanda ya tabbatar wa da Akoko faruwar lamarin, ya ce, rundunar Hisbah ta gurfanar da Elijah a gaban kotu a ranar Talata, 2 ga watan Fabrairu, daga nan kuma aka tura shi gidan yari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button