News

An cafke mutanen da suka daka wawuso a kantin da gobara ta tashi a Abuja, Wanda Hakan Yasa Sheikh Isa Ali Pantami Kuka,

An cafke mutanen da suka daka wawuso a kantin da gobara ta tashi a Abuja, Wanda Hakan Yasa Sheikh Isa Ali Pantami Kuka,

Jami’an tsaro sun cika Hannu da mutanen da suka yi Wawason Dukiyar Al’umma a katafaren kantin Abuja, Mai Suna Next Cash’N Carry, wanda gobara ta kone a safiyar Yau Lahadi.

Kamar Yadda Kuke Gani Cikin Hotuna, wadannan sune wadanda Ake Zargi Da Satar Kayayyakin wajen.

Satar Kayayyaki A Katafaren Kantin Yayin Da Yake Ci Da Wuta, Ya Dagawa Sheikh Pantami Hankali, Lamarin Da Ya Sanya Shi Zubda Hawaye.

Gobara ta ƙone kantin Next Cash & Carry a Abuja

Gobara ta ƙone ɓangarorin ɗaya daga cikin kantina mafi girma a Abuja babban birnin Najeriya, Next Cash and Carry.

Wutar ta mamaye katafaren kantin da ke yankin Jahi da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Lahadi, a cewar rahotanni.

Hotunan da suka fito daga wurin sun nuna yadda ma’aikatan kashe gobara ke ƙoƙarin kashe wutar yayin da baƙin hayaƙi ya tokare sararin samaniya.

Sai dai ba a san abin da ya haddasa gobarar ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

An rufe babban titin da ke kaiwa ga kantin yayin da ‘yan kwanakwana ke ci gaba da aikin kashe gobarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button