News

An Tura Matashi Gidan Yari Saboda Yayi Amfani da Kudin Maigidansa Wajen Ceto Rayuwar Mahaifiyarsa

An Tura Matashi Gidan Yari Saboda Yayi Amfani da Kudin Maigidansa Wajen Ceto Rayuwar Mahaifiyarsa

An Tura Matashi Gidan Yari Saboda Yayi Amfani da Kudin Maigidansa Wajen Ceto Rayuwar Mahaifiyarsa.

An aike da matashi mai suna Isa Abubakar Saddik zuwa gidan kurkukun Kurmawa da ke birnin Kano sakamakon korafi da maigidansa ya kai wajen hukuma yana mai cewa ba zai dauki asara ba lallai sai an biya shi kudinsa dubu dari hudu da sittin 460k wanda aka yi amfani da su wajen ceto rayuwar mahaifiyar yaronsa mai suna Isah Abubakar Saddiq.

Isah Abubakar Saddik wanda maraya ne mahaifinsu ya rasu kuma shi ne ke daukar nauyin mahafiyarsa da kannensa mata, yana aiki a karkashin maigidansa a shagon siyar da suminti da ke unguwar jaen, kuma matashi ne mai hazaka da amana. Wata rana kwatsam mahaifiyarsa ta kamu da mummunar cuta kamar za ta mutu, wanda matashi Isa ya yi ta dawainiyar kudaden asibiti da magani bayan watanni Allah ya sa ta mike ta sami lafiya sai dai Isa ya yi amfani da dukiyar maigidansa saboda halin damuwa da ya shiga na ceto rayuwar mahaifiyarsa da zummar komai idan ya yi satil zai dawo da kudin.

Daga baya ne maigidansa ya bukaci ya biya shi kudinsa wanda ya kai shi wajen ‘yan sanda daga nan sai kotu, daga Kotu kuma aka tura shi Kurkukun Kurmawa.

Masu neman karin bayani za su iya kiran wannan lamba 09122966053.

Masu son bin diddigin lamarin don samun tabbaci za su iya zuwa Kotun Kofar Kudu wacce Ibrahim Sarki Yola ke alkalanci, an yi shari‘ar ne a ranar laraba talatin ga watan November da ya wuce, sunan wanda yake kara Nafiu Muhammad Alhasan.

A yanzu haka Isa yana Kurkukun Kurmawa cell 3, gidansu Isa yana unguwar Ja’en layin gidan kallon bol daidai kantin attakawa gidansu Maryam za a sami mahaifiyarsa a gidan ko kuma ta wannan lamba; 090

Allah Ya Kyauta na gaba Mun gode da Ziyartar wannan Shafi namu wanda yake kawo maku labarai da dumi duminsu Mungode

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button