News

Arha banza na sameta, sadaki N400 na biya, shi ma sadaka na yi a coci, Mijin Baturiya mai shekaru 70

Wani Mijin Baturiya mai shekaru 70 Yace A Arha banza Ya sameta, sadaki N400 Ya biya, shi ma sadaka Ya yi a coci,

Bernard Musyoki ya kara da cewa Ya hadu da Deborah Jan Spicer mai shekaru 70 a Kafar Sadarwa Ta Facebook A shekarar 2017 wanda suka fada tafkin soyayya.


A ranar 29 ga watan Disamban ne A Shekarar 2020 Baturiyar mai shekaru saba’in tayi Tattaki Ta nufi har kasarsa (Kenya) domin ganin masoyinta kuma bayan wata Guda su ka yi aure.

Arha banza na sameta, sadaki N400 na biya, shi ma sadaka na yi a coci, Mijin Baturiya mai shekaru 70

Musyoki ya ce bayan gabatar da ita ga iyayensa sun soki auren inda su ka ce ba za ta iya haihuwa ba don ta yi masa tsufa tunda shekarun ta sun lula


Bernard Musyoki mai shekaru 35 ya bayyana farincikinsa na auren matar da ta nunka shekarunsa kuma soyayyarsu ta gaskiya ce, a cewarsa.

Yayin da fitacciyar jaridar Kenya ta TUKO.co.ke ta yi hira da shi ya bayyana cewa:

“A Facebook mu ka hadu kuma ni na tura mata gayyatar zama kawata ta amince. Cikin mako daya na bukaci ko za ta iya aure na ta kuma amince.”

A cewarsa ya dinga kokarin zuwa Amurka don ganinta amma abin ya ci tura har sai da dai tazo su ka hadu.

Batun kuwa sadaki ya ce ya samu arha don dala daya (N409.89) ita da yaranta su ka nema a wurinsa, shi ma cewa su ka yi ya yi sadaka a coci.

Duk da yadda gidanmu yake kamar mashekarar jaki, a haka kyakkyawar budurwata take so na, Saurayi
Wani matashin saurayi dan kasar Ghana mai amfani da suna unrulymacmonies, kuma yana amfani da bra_kingsley1 a manhajar TikTok, ya shayar da mutane da dama mamaki.

A bidiyon kyakkyawar budurwarsa wacce ya wallafa a TikTok, ya ce haka nan budurwarsa take sonsa.
An ga yadda budurwar ta shiga gidansu wanda yake kaca-kaca duk kwata har bakin kofar dakinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button