Autan Marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero Ya Auri Mata Biyu A Rana Ɗaya

A Jiya Lahadi Ne Aka Daura Auren Autan Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero, Wato Mustapha Ado Bayero.

Mustapha Dai Shi Ne Dan Auta a cikin ‘Ya’ya 63 Na Marigayi Mai Martaba Marigayi Sarki Ado Bayero.

Mustapha Kani Ne Ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Allah Ya Ba Su Zaman Lafiya Da Zuri’a Dayyaba!

Daga Jamilu Dabawa

Click Here To Drop Your Comment