News

BABBAN MAGANA BIDIYO: Zulum yasa a zane wani talaka don yabi layi zai karbi tallafin da za a raba,

BABBAN MAGANA: Zulum yasa a zane wani talaka don yabi layi zai karbi tallafin da za a raba,

-anyi kira ga kungiyar yancin dan Adam ta hukunta Zulum kan cin zarafin wannan matashi….

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sa a zane wani matashi saboda ya bi layin karban tallafi da Gwamnan zai rabar.

Muryoyi ta ruwaito an ga yadda Gwamnan ya tsawatawa matashin cewa ya tashi ya fita sannan yasa ayi masa bulala da duk matasan da suka shiga layin wadanda za ayiwa rabon tallafin.

Wannan lamari bai yiwa wasu dadi ba inda suke cewa anci zalin matashin wasu kuma na cewa ya kamata yan kungiyar kare yancin dan Adam su tuhumi Gwamnan kan yadda zai tozarta matashin don kawai zai karbi hakkinsa.

“ai kayan na Gwamnati ne kuma shima matashin dan kasa ne” to menene na sakawa a dake shi? Wasu kuma na cewa Boyayyen mugun halin Zulum din ne ya soma fitowa fili tunda yana nunawa talakawa kyara sai dai wasu sun nuna nasu mabanbantan ra’ayin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button