Babban Mai ‘Kera Boma-Bomai na Kungiyar Boko Haram, Musa Adamu Ya Mika Wuya.

Babban Mai Kerawa Kungiyar Boko Haram Boma Bomai Musa Adamu Wanda aka fi Sani da Mala Musa Abuja,

Shida Mataimakinsa Usman Adamu wanda aka fi Sani da Abu Darda sun Mika wuya ga Jami’an Tsaro.

Sun dai mika wuyan ne tare da Iyalansu da Mabiyansu a Karamar Hukumar Bama, Jihar Borno

Mukaddashin Kwamandan (GOC) Sashi na 7 na Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Abdulwahab Adelokun Eyitayo ne ya karbe su a hedkwatar 21 ta Special Armored Brigade dake Bama a ranar Asabar, 7 ga Agusta, shekarar 2021

Click Here To Drop Your Comment