News

BATUN HANEEFA: Ɗan sanda ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi 10 a kan Abdulmalik Tanko a kotu

Hanifa: Ɗan sanda ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi 10 a kan Abdulmalik Tanko a kotu

Ubale Usman, wani ɗan sanda kuma shaida a kan zargin kisan da Abdulmalik Tanko ya yi wa Hanifa Abubakar, ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi har guda goma a kotu.

A ci gaba da Shari’ar, wacce a ke yi a babbar kotun Kano mai lamba 5, lauyan gwamnati, Antoni-Janar na Jihar Kano, Musa Lawal ya gabatar da shaidu uku wanda a ciki har da Usman a matsayin Mai shaida na 3, PW3.

Usman, wanda jami’in bincike ne a sashin yaƙi da garkuwa da mutane na Rundunar Ƴan Sanda ta Kano, ya gabatar da kayan shaidar aikata laifin da su ka haɗa da wayoyin salula, rigar sanyi, farin hijabi, bajon makaranta, shebir, hoton Hanifa, kuɗi Naira 30,300 da sauran su.

Usman ya bada shaida cewa a ranar 4 ga watan Disamba, 2021 rundunar ƴan sanda ta karɓi ƙorafin ɓatan yarinya da ga baban marigayiya Hanifa.

Ya ƙara da cewa a ranar 20 ga watan Janairu, Hukumar Ƴan Sandan Farin Kaya, DSS, ta sanar wa da Rundunar Ƴan Sanda cewa an kama Tanko da laifin yin garkuwa da Hanifa.

Usman ya ƙara da cewa, da ga bisani, jami’an DSS da na ƴan sanda su ka garzaya inda Tanko ya binne Hanifa a unguwa Tudun Murtala, a Kwantar Ƴan Ghana inda a ka haƙo gasar Hanifa.

Usman ya shaida wa kotu cewa shi da kan sa ya tuhumi Tanko, wanda ya kuma amsa laifin cewa shi ya shi ya yi garkuwa da Hanifa ran 4 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 5:30 na yamma yayin da ta ke dawo wa da ga Islamiyya.

Ya kuma bada bayanan yadda Tanko ya ɓoye Hanifa a gidan sa, da ƙaruwar da ya yi wa matarsa cewa ƴar ma’aikaciyar sa ce ta tafi Abuja yin jarrabawar ɗaukar aiki, da dai duk sauran bayanai.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Usman Na-abba, ya bada umarnin a maida Tanko da Hashimu Isyaku da Fatima Musa gidan yari, inda za a ci gaba da sauraron ƙarar a yau Alhamis, 3 ga watan Maris.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, wancan zaman da a ka yi, Tanko da abokan aikata laifin duk sun nisanta tuhume-tuhumen da a ke musu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button