News

BIDIYO: A jihar Kano an tsinci gawar wani matashin mai suna Ghaddafi a cikin kwata

A jihar Kano an tsinci gawar wani matashin mai suna Ghaddafi a cikin kwata

An tsinci gawar wani matashi mai kimanin shekaru 25 mai suna Ghaddafi Saleh a cikin wata kwata da safiyar Laraba a Jihar Kano.

Lamarin ne a unguwar Kundila kan titin Zariya daura da asibitin dabbobi.

A zantawar Aminiya da wani matashi kuma mazaunin yankin, Sultan Bello, ya ce ruwa ne ya koro gawar mutumin ya kawo ta wannan waje.

Ya kuma ce, “Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake tsintar irin wannan gawar, na uku ke nan cikin kwanaki hudu da suka wuce.”

A nasa bangaren, mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da rasuwar matashin, inda ya ce tuni suka mika gawar ga ofishin ’yan sanda da ke Titin na Zariya Road a Kano.

Ya kara da cewar mamakon ruwan da aka yi ranar lahadi shi ne musabbabin faruwar hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button