Kannywood News

BIDIYO: A Taimake Ni ‘Ya’yan Sarkin Kano Za Su Halaka Ni, Cewar Matar Ɗandarman Kano Hauwa Bello Ado Bayero

A Taimake Ni ‘Ya’yan Sarkin Kano Za Su Halaka Ni, Cewar Matar Ɗandarman Kano Hauwa Bello Ado Bayero

Tsohuwar jarumar Kannywood, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Ibrahim, na neman agajin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da sauran jama’a kan halin ha’ula’in da ta ke ciki

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Lokacin da ta ke fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, sunan ta Maijidda Ibrahim, yanzu kuma Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero. Ta na ɗaya daga cikin ɗimbin mata ‘yan fim da su ka yi aure kuma su na zaune a gidan miji. Tsawon shekaru 21 kenan tun da tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Khusufi saboda wani fitaccen fim na Ali Nuhu da ta taɓa yi, ta ke zaune a gidan mijin ta mai suna Alhaji Bello Ado Bayero, wanda shi ne Ɗandarman Kano a yanzu, kuma ɗaya daga cikin ‘ya’yan Mai Martaba Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero. Allah ya albarkaci auren nasu da ‘ya’ya shida, mata biyu da maza huɗu.

Sai dai ka kash! ashe dai ganin kitse ake wa rogo. Masu sha’awar cewa Hauwa Bello Ado Bayero na kwance a cikin daula ba su san cewa kamar a kan ƙaya ta ke zaune ba saboda wani mugun yanayi da ta samu kan ta a ciki a tsawon shekaru aƙalla 15. Yanayi ne wanda ta daɗe ta na ɓoyewa har zuwa yanzu da ta ga uwar bari ta yanke shawarar ta sanar da duniya irin halin ha’ula’in da ita da ‘ya’yan ta su ke ciki domin gudun abin da ka je ya dawo, wato kada sai ita ko mijin ta wani ya ƙaura wata ƙurar ta tashi, a riƙa cewa to me ya sa ba ta faɗa ba tun tuni?

Hajiya Hauwa dai ta kasance cikin wannan ƙangi mai hana barci ne ba domin komai ba sai saboda wai ita ‘yar fim ce a da, sannan kuma ba ta da kowa a dangin ta wanda ya isa ya ƙwatar mata ‘yancin ta. Shin me ya faru?

Tsohuwar jarumar ta tattauna da mujallar Fim (da izinin mijin ta) a ranar Laraba, 11 ga Mayu, 2022 saboda a kai mata agajin gaggawa ita da yaran ta. Ga yadda zantawar su da wakilin mu na Kano, MUKHTAR YAKUBU, ta kasance;

FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga jama’a.

HAUWA BELLO ADO BAYERO: To, assalamu alaikum. Suna na Hauwa Bello Ado Bayero, wadda ake ce wa Maijidda. Ni ce matar ɗan Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero ce, wanda ya riƙe matsayin Hakimin Kura, wato Alhaji Bello Ado Bayero. A ‘ya’yan Sarki shi ne na goma a maza. Yanzu ba ya hakimi, amma ya na nan a matsayin sa na Ɗandarman Kano.

FIM: Yaya rayuwar ki ta kasance kafin auren ki?

HAUWA BELLO ADO BAYERO: To, kafin na yi aure, na yi fim a industiri. A (harkar) fim ɗin ya gan ni ya ce ya na so na kuma ya aure ni. A shekarar 2001 ya aure ni. Saboda haka yanzu in aka lissafa shekara 21 kenan. Saboda haka, ya aure ni, mu ke zaune da shi a cikin aminci, a cikin zaman lafiya tsakani na da shi.

Allah ya yi mana zuri’a, na haifi ‘ya’ya shida da shi – mata biyu, ina da maza guda huɗu da shi. Ta farko sunan ta Mama (Hasiya), na biyu akwai Muhammadu Tukur (sunan sa Maje), na uku Sultan (shi ne Ado Bello Ado Bayero); sannan ina da Ridwan, sannan kuma ina da Ali, sannan kuma ina da Azeeza. Akwai ‘ya ta da na ke riƙe da ita, sunan ta Shaheeda. Su bakwai ne a hannu na, amma shi nashi sosai ‘ya’yan sa shida ne.

FIM: Ya ku ke da ‘yar ki da ki ka ce ba tasa ba ce?

HAUWA BELLO ADO BAYERO: ‘Ya ta da na ke riƙe da ita ‘yar wa na ce. Tun ta na yarinya, shekarar ta biyu, na je na ɗauko ta. Mahaifin ta da ni cikin mu ɗaya da shi, na ke riƙe da ita, ta na hannu na, na haɗa ta da ‘ya’ya na. Yanzu ma matsala ce ta tashi na ke gaya wa duniya saboda abin da ake yi min.

FIM: Shekarun ‘ya’yan ki nawa?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: E. Shekarar Hasiya 17 yanzu. Shi kuma Tukur ya na da shekara 15. Shi kuma Sultan ya na da shekara 13. Shi kuma Ali ya na da shekara 10. Shi kuma Ridwan ya na da shekara 7. Sannan ita Azeeza ta na da shekara 4.

FIM: Wace matsala ki ke fuskanta yanzu?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: Rayuwa ta yi min tsauri, rayuwa ta yi min tsanani. Da ma a gidan Sarkin Kano Ado, ni babu mai so na in ba shi marigayi ba; shi ya ke so na, shi ne ya nuna min cewa ni mutum ce kuma daidai na ke da ‘ya’yan sa. Saboda tun da na ke zuwa gaban sa in gaishe shi, in je in nemi alfarma kuma ya yi min, bai taɓa nuna min wani bambanci tsakani na da ‘ya’yan sa ba. Amma tun ranar da aka kawo ni gidan Sarkin Kano Ado, ‘ya’yan sa mata su ka sa ni a gaba. Ba sa ƙauna ta, ba sa so na.

Akwai Rabi, ita ce ake ce wa Rabin Daura; ita ce surukar Bashar Mai Daura; ɗan sa ya rasu, soja ne, ya yi hatsari a hanya; matar sa. Ita ce yayar Siyama.

Sannan akwai Hauwa Lele; ita ce wadda Madakin Kano ya taɓa aure; da ‘ya’yan su. Ita ma ‘yar Sarkin Kano ce marigayi. Su su ka saka ni a gaba. Su su ka taɓa zuwa gida na, har cikin tsakiyar gida na, su ka yi mini duka, su ka zage ni, su ka wulaƙanta ni. Lokacin Sarkin Kano Ado ya na da rai, Allah ya jiƙan sa, Allah ya gafarta masa. Ciroman Kano ya kira mu ya zaunar da mu ya yi mana sulhu, ya ba ni haƙuri, ya ce min in yi haƙuri.
Duk da haka ba su ƙyale ni ba. Su na ta yi min bi-ta-da-ƙulli dukan kabarin kishiya! Duk inda na zauna waɗannan da na ke faɗa – ƙananan (‘ya’yan Sarki), ban da manyan, don ni ban da abin da zan ce wa manyan ‘ya’yan Sarkin Kano mata sai godiya; kamar Giwa, ta na mutunta ni, ta na so na; kamar Nana Musan Musawa, ita ma ta na mutunta ni, ta na girmama ni; Yaya Balaraba; to ɗaiɗaikun su, gaskiya babu abin da zan ce masu. Amma ƙananan, ban da abin da zan ce masu…
To yanzu abin ne da ya yi tsamari ne har na fito na ke gaya wa duniya, na ke nema a taimake ni, a rufa mini asiri. Ina so mutane su gane matsalar da na ke ciki.
An yi Hawan Panisau (na Ƙaramar Sallah ta 2022), na je gidan Sarkin Kano in gaida Sarki tunda Sarki uba na ne, ubanɗaki na ne, na yi uba da shi. Na je in gaishe shi, gaisuwa irin ta ban-girma. Sai yar miji na, su su biyu – ana ce wa ɗayar Yaya Meri, ɗayar ana ce mata Gwaggon Rano – ina zaune sai ta kwaɗa min kira, ita yar miji na, ta ce in zo ta na kira na. Na je. Fuskar ta babu yabo ba fallasa. Ina zuwa, sai ta ce min in je ɗakin ƙanwar ta; ƙanwar tata ita ce yar miji na, ana ce mata Gwaggo Sarai. Ta ce in je in jira ta a ɗakin.
Na tafi ɗakin na zauna. Ina jiran su, sai ga su sun shigo. To lokacin da na shiga ɗakin, akwai matar Sarkin Ƙaraye a zaune, da ‘yar ta babba; da ita yar miji na, ana ce mata Gwaggo Sarai, ita ma da ‘yar ta, na same su a ɗakin, na zauna, sai ga yar miji na da ta kira ni ta ce in shigo, ta shigo. Sai ta ce min in shigo cikin ɗaki. Na shigo cikin ɗakin. Sai ta ce min, “Hauwa.” Na ce mata, “Na’am.”

“Me ya haɗa ki da Yaya Fati har ki ka zage ta?”
Sai na ce mata, “Wacece Yaya Fati?” saboda na manta; gidan Sarkin Kano akwai Fati da yawa.

Sai ita ƙanwar miji na sai ta ce min, “Don kutumar …, don bu…, ke har kin manta wacece Yaya Fati? Don kutumar bu…, shegiya, talaka, matsiyaciya, har kin ci kin ƙoshi da za ki manta wacece Yaya Fati?”

Sai ni ma sai na miƙe na ce, “Ni ki ke wa wannan zagin? Me na yi miki ki ke min wannan zagin?”

Kafin in gama magana ta rufe ni da duka. Ni ma sai na zage ta. Zagin da na yi mata, gaba ɗaya sai su ka yo kai na, su yayyen nan nasa waɗanda na ke gaya maka su na ɗakin, sai su ka yo kai na, wai don me ya sa zan zagi Sarki? Na ce, “Ni ai ba Sarki na zaga ba.”

Ta na ta duka na, ta na duka na, ta yaga min kaya. Na riƙe ta sosai. Da ma ta riga ta yaga min kaya. Su kuma ba su raba mu ba. Saboda haka sai ta kama min gashi, ta tsinka min gashin tsakiyar kai na. Kawai sai na zama ‘collapsed’. Sai na ji kamar an zare min wani abu a cikin rai na. Sai na faɗi, ina cewa su ba ni ruwa, su ba ni ruwa in sha!

Karanta kuma Rarara ya shirya rugunɗumin wasan Sallah na mako ɗaya a ƙarƙashin 13×13 a Kano

Sai ita matar Sarkin Ƙaraye ta ce a ɗauko mata ruwa. Ita ta tallafa ni, ita ta ba ni ruwa, ta zuba min ruwan. Amma wannan Gwaggon Rano – ita ce matar Hakimin Rogo – ba ta daina zagi na ba, ta na kai na, za ta dake ni. Ragowar ‘ya’yan Sarkin duk sai su ka zo, sai su ka shigar mata, su na zagi na.

Na fita a gigice. Haka na fita Sararin Garke, tsakar gidan Sarki, ga dogarai ga kowa, riga na a yage, ina ihu ina kuka, ina: “A taimake ni ‘ya’yan Sarkin Kano za su kashe ni!”
Aka kai ni wani ɗaki aka rufe ni, aka lallaɓa ni. ‘Yar Sarkin Kano, babbar ‘yar sa (Yaya Fati), ita ta ɗauki riga abaya ta ba ni don na suturta jiki na.

Saboda haka, ina neman taimako. Abin ya yi yawa! Saboda ba sa jin maganar na gaba da su.
Na je gaban Kwamishinan ‘Yan Sanda na kai ƙara. An kira su, ba su zo ba. To yanzu ni na rasa yadda zan yi.

Lokacin da Sarki ya zauna, na je don na gaishe shi. Amma ya na gani na ya ce, “‘Ya ta, me ya faru na gan ki a haka?”Na ce, “Sarki babu komai.”

Daga ƙarshe da ya matsa na ke sanar da shi, “Ina neman taimako, za a kashe ni.” Na faɗa masa abin da ya faru.

Don haka ya sa a kira su don ya san abin da ya ke faruwa. Amma bayan an kira wadda ta yi mini dukan sai da aka shafe sama da minti talatin ba ta zo ba, sai da aka koma aka sake kiran ta.

To, bayan ta zo ne Sarki ya ce me ya sa ta yi mini haka? Sai ta ce na zagi Sarki ne shi ya sa ta dake ni.

Nan take Sarki ya ce, “Haka kawai ba za ta zagi Sarki ba, sai dai idan kun yi mata wani abu.” Don haka Sarki ya yi mana faɗa, ya ce mu je mu zauna lafiya. Amma har a gaban sa sai da su ka tayar da hayaniya, su na zage-zage.

FIM: Yaya wannan matsalar ta shafi rayuwar ‘ya’yan ki?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: To rayuwar ‘ya’ya na, kullum sheganta mini ‘ya’ya su ke yi, su na cewa ‘ya’ya na shegu ne, Allah ya tsine wa ‘ya’ya na albarka, su ba su san darajar ma ‘ya’ya na ba, wai ‘ya’ya na ‘ya’yan industiri ne, kullum maza ne su ke nema na! Abin da kullum su ke gaya min kenan. To ni abin da ya ba ni tsoro kenan na fito duniya na ke faɗa. Su na sheganta min ‘ya’ya na, su na faɗa su na ce wa ‘ya’ya na shegu.

Yanzu haka ina da ‘voice’ ɗin (ɗaya daga) cikin su wadda na gaya maku, Rabi, ina da ‘voice’ ɗin ta da sheganta min ‘ya’ya, ta tsine min ‘ya’ya na. Ina nan da ‘voice’ ɗin ta, kuma za a saka kuma za ku ji ‘voice’ ɗin nata da abin da ta ke faɗa, da irin zagin da ta ke min, ta ke aibanta ni, ta je aibanta min zuri’a ta.

FIM: Yaushe wannan matsalar ta soma?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: Haka su ke min tun farko. Tun lokacin da na ce maka sun zo sun dake ni. Ɗa na a lokacin shi ne na ce maka shi ne na biyu, shi ne shekarar sa 15 ɗin da na gaya maka. To a lokacin ya na da wata uku su kai min wannan abin. Watan sa uku a lokacin a duniya. To yanzu zancen da na ke maka shekarar sa 15, su ke min haka, su ke aibata ‘ya’ya na, kullum (su na cewa) ‘ya’ya na ba ‘ya’yan miji na ba ne.

To, ni abin da ya sa na fito na ke gaya wa duniya, na ke gaya wa midiya, Allah shi ya san gawar fari tsakani na da ni da shi, ban san me su ka shirya ba bayan rasuwar sa. Kada wani abu ya zo ya same – shi ma sun sa shi a gaba – wani abu ya zo, ko bugun zuciya, ko wani abu ya zo ya same shi, ko su ce na kashe shi ko su ce wani abu, su ce ‘ya’ya na ba ‘ya’yan sa ba ne. Shi ne na ke nema duniya ta taimaka min.

FIM: Yaya alaƙar ki da Sarkin Kano ta ke a yanzu?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: Rayuwar aure na lafiya lau. Ban da abin da zan ce wa Sarkin Bichi, ban da abin da zan ce wa Sarkin Kano, ba abin da ba su yi min a rayuwa tsakani na da su. (Amma waɗannan matan) sun fi ƙarfin su, ba sa jin maganar su. Tun mahaifin su ya na da rai su ke yi mini wannan abin.

FIM: Wane taimako ki ke nema?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: So su ke su hana ni zaman aure, kuma so su ke su yi ‘frustrating’ ‘ya’ya na. Saboda haka, ina nema a taimake ni a yi min tsakani da ni da su. Da ma ba na zuwa gidan su, amma duk da haka ba su ƙyale ni ba, su na zagi na, su na aibanta ni. Yanzu ban isa in shiga cikin al’amarin su ba.

FIM: Ba ki mu’amala da su?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: Ba wata mu’amala. Abin da ke haɗa ni da su biki. In za a yi biki, wanda ya ke so ya kawo min, zan je. To a nan ne in sun gan ni sai su aibanta ni, su zage ni, su ɓata ni saboda ni ‘yar fim ce. A kullum a ‘yar fim su ke zagi na. Kuma ‘voice’ ɗin da za a sa ma ai mutane za su shaida, su ji yadda su ke zagi na a kan fim. Shekara ta nawa rabo na da fim, iye? Mu’amala ce dai da ni da ‘yan fim, wanda zai yi da ni zan yi da shi saboda ai mutane ne; akwai wanda mu ka zauna da su mu ka yi mu’amala da su, mu ka yi zaman arziki da su. Saboda haka duk wanda ya gayyace ni mu’amalar sa, zan je. Saboda haka ba zan ce wani mu’amala na ‘yan fim ko na wani abu ba zan yi ba. Ina zuwa ina gaishe su, su na zuwa su na gaishe ni.

FIM: Me ki ke buƙata yanzu?
HAUWA BELLO ADO BAYERO: To, ni saƙo na, abin da na ke so in gaya wa al’umma, mu a kullum da ake zagin mu, ake aibata mu a ‘yan fim, ake ce mana shegu, ake zagin mu, ake cewa ba ma zaman aure, to irin wannan rayuwar (tawa), yanzu in ba ka da nisan zuciya, ba ka da tawakkali, ba dole ka fito ba, iye? Mijin ka ya bar ka ka zauna lafiya, dangin miji sun fi su su nawa sun hana ka ka zauna lafiya, sun saka ka a gaba, ba irin aibata ka a duniya da ba sa yi. In su ka gan ni su ce min, “‘Yar tasha, shegiya, karuwa! ‘Yar fim, ragowar ‘yan fim!” Kullum a haka na ke.

To, ni na san abin da na ke tunani, tunda ni na san ƙarfi na da iko na da wani abu na ba shi ne ya kawo ni gidan Sarkin Kano Ado ba. Ina ‘yar wasan Hausa, sun ce ni ‘yar talaka ce ina ‘yar talaka, ni ba ‘yar kowa ba, Allah ya tsamo ni a cikin ‘yan fim ɗin, ya kawo ni gidan Sarkin Kano, to na san Allah ne ya kawo ni. Amma wani bai isa ya fitar da ni daga cikin gidan miji na ba! Saboda haka, ni na yi imani da Allah, na yi imani da Manzon Allah (S.A W.), na yi imani da ranar mutuwa ta, saboda haka wulaƙanci dai ne da tozarci kuma da aibata min ‘ya’ya da sheganta min ‘ya’ya da ake, na gaji!

Shi ne na ke neman al’umma ta taimaka min, ta taimake ni ta shiga cikin al’amarin nan, ta shiga tsakani na da wa’innan mutanen, su ƙyale ni da ni da ‘ya’ya na mu zauna lafiya. Assalamu alaikum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button