Kannywood News

BIDIYO: Allah Sarki Cikin Wani Yanayi Madagwal Yayi Wata Magana Mai Taba Zuciya Kan Batun Da Ake Yadawa Ya Mutu

BIDIYO: Allah Sarki Cikin Wani Yanayi Madagwal Yayi Wata Magana Mai Taba Zuciya Kan Batun Da Ake Yadawa Ya Mutu

Fitaccen Dan Wasan Barkancin Nan Kuma Jarumi A Masana’antar Kannywood Wato Ali Artwork.

Ya Fito Ya Karyata Wani Labari Dake Yawo A Shafukan Sada Zumunta Na Cewar Ya Rasu.

A Safiyar Ranar Asabar Ne, Aka Tashi Da Rade Radin Rasuwar Jarumin A Shafukan Sada Zumunta.

Jama’a Da Dama Sun Kado Tare Da Nuna Alhinin Rasuwar Tasa, Yayinda A Gefe Guda Kuma Wasu Ke Karyatawa.

Kasancewar An Saba Yiwa Jaruman Kannywood Karyar Mutuwa, Hakan Tasa Wasu Ke Ganin Kamar Shima Dai Karyar Ce Ta Biyo Ta Kansa.

Hakan Tasa Abokan Sana’ar Tasa Suka Ankarar Dashi Wannan Labari Dake Ta Yaduwa A Kafafen Sada Zumunta.

Lamarin Da Yasa Jarumin Fitowa Acikin Wani Dan Karamin Bidiyo Da Ya Wallafa A Shafinsa Tare Da Karyata Wannan Jita Jitar Inda Yake Cewa.

“Allah kasa mu cika da imani 🤲 dan Allah jama’a mu guji yada jita jita wallahi ni ina nan lafiya ta kalau ko ciwon kai bamba amma na tashi da safe wai ana cewa na mutu wallahi wannan maganar ba gaskiya bace kuma in lokacin mu yayi insha Allah zamu tafi domin MUTUWA tana kan kowa fatan mu shine Allah ka mana KYAKYAWAN karshe Darajar shugaban mu Annabi Muhammadu S.A.W 🤲💚🤲”

Gadai Bidiyon Ku Kalla

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button