News

Bidiyo An gano wani mutum da aka kulle a cikin daki tsawon shekaru 20 a jihar Kaduna.

Bidiyo An gano wani mutum da aka kulle a cikin daki tsawon shekaru 20 a jihar Kaduna.

Jami’an kare muhalli sun gano wani mutum da aka kulle a cikin daki tsawon shekaru ashirin a jihar Kaduna, A cewar jaridar Nigerian Tribune, jami’an sun gano mutumin ne a wani gida a titin Benin, a tsakiyar birnin Kaduna a yau Laraba, 12 ga watan Oktoba.

Yola24 ta rawaito cewa, Kakakin nasu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun kadu matuka da gano lamarin.

“A yau mun zo gidan nan ne domin neman abubuwan sha da aka saba ajiyewa a gidajen zama ba tare da ingantaccen wurin ajiya ba sai muka ga wani tsirara a kulle a daki,” inji shi.

“Mun gano cewa yana cikin wani yanayi mara dadi, kamshin da ke fitowa daga dakin ya kasa jurewa.

“Daga baya sai muka fasa dakin muka fito da shi, yana cikin hali irin na dabba, daga nan ne muka samu labarin an ajiye shi a dakin tsawon shekara ashirin.

“Mun kuma gano an ciyar da shi a daki, yana fitsari ya wuce najasa a daki daya.

“An gayyaci ‘yan sandan Magaji Gari da ke tsakiyar yankin Kaduna ta tsakiya daga bisani suka tafi da shi.” Ya kara da cewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button