News

BIDIYO: An Hallaka Ƴan Bindiga Suna Tsaka Da Rabon Kuɗin Fansar Da Suka Amsa

BIDIYO: An Hallaka Ƴan Bindiga Suna Tsaka Da Rabon Kuɗin Fansar Da Suka Amsa

An kashe wasu masu garkuwa da mutane a yayin da suke tsaka da rabon kudin fansa a maboyarsu a cikin daji.

Jami’an tsaro sun aika ’yan bindigar lahira ne a musayar wuta a wani daji a Karamar Hukumar Moro ta Jihar Kwara, ranar Talata da dare.

An ritsa bata-garin ne a maboyarsu, suna cikin raba kudin fansar matar da dan dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kwara a Jam’iyyar APC, Honorabul Lawal Ayansola Saliu, wanda aka fi sani da LAS.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce, “’Yan sanda da ’yan banga da mafarauta ne suka ritsa bata-garin suna tsaka da rabon kudin da suka karba daga iyalan mutanen da suka sace.

“Bata-garin sun bude wa jam’ian tsaron wuta, inda a yayin musayar wuta aka kashe biyu daga cikinsu, kamar yadda likitoci suka tabbatar bayan an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori (UITH).”

Okasanmi ya ce an kwace wata mota kirar Honda Accord da wata bindiga daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ya kara da cewa ana bin sawun ragowar da suka tsere domin su girbi abin da suka shuka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button