News

BIDIYO: An Kashe Matar Aure A Gidan Ta Na Aure Dake Kano Ana Zargin Cewar Yan Fashi Ne Suka Buga Mata Tabarya

BIDIYO: An Kashe Matar Aure A Gidan Ta Na Aure Dake Kano Ana Zargin Cewar Yan Fashi Ne Suka Buga Mata Tabarya

An kashe matar aure a cikin gidanta a Kano

Mutanen unguwar Danbare da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano sun shiga tashin hankali da alhini bayan da a ka iske an kashe wata matar aure, mai suna Rukayya Mustapha a cikin gidan aurenta.

Daily Nigerian ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a yammacin Asabar, inda makasan na Rukayya su ka kuma ji wa ƴaƴanta biyu ƙanana rauni.

Wannan jaridar ta kuma jiyo cewa an yi amfani da taɓarya ne a ka buga wa marigayiyar a kanta, inda ta ce ga garin ku nan.

Ba a san ya a ka yi makasan su ka shiga gidan ba duk da cewa, an ce a kwai wasu masu aikin gini a maƙotan gidan da abin ya faru.

An ce ba wanda ya san mai ya faru har sai da mijin ta ya dawo da ga kasuwa sannan ya tarar da ita a kwance ta mutu.

Da wakilin mu ya kira Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai samu ya amsa wayar ba.

Sai dai kuma BBC Hausa ta rawaito cewa SP Kiyawa ya ce rundunar ta kama mutane biyar da a ke zargi da hannunsu a kisan.

https://youtu.be/1cSGsPy4Fsc

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button