News

BIDIYO: Bayan Kwana Daya Da Yaje Har Kabarin Ta Ya Zage Ta Allah Ya Nuna Isharar Sa

BIDIYO: Bayan Kwana Daya Da Yaje Har Kabarin Ta Ya Zage Ta Allah Ya Nuna Isharar Sa

Kwana Daya Da Faruwar Wani Lamari A Jahar Kano, Wanda Ya Daga Hankalin Al’ummar Nigeria Baki Daya.

Lamarin Da Akaga Wani Dan Hansin Yaje Kan Kabarin Wata Mata Inda Ya Raba Kafa Ya Ringa Zaginta.

Saboda Wai Dan Matar Yaje Gidan Su Ya Zagi Mahaifiyar Sa, Shine Shima Yaje Kan Kabarin Babarsa Ya Rama.

Tuni Dai Rundunar Yan Sanda A Jahar Kano, Ta Sanar Da Chafke Wannan Dan Hansin Wanda Ya Aikata Wannan Jahilci.

A Ta Bakin Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sandan Jahar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa Ya Sanar Da Cewa.

Rundunar Yan sanda a Jihar Kano sun Kama matashin Nan da ya raba kafa akan kabari Yana surfawa wata dattijuwa zagi sabida sunyi fada da Yar data Haifa Kuma Yana dauka a bidiyo.

A yau Lahadi ne a ka tashi da ganin wani faifan bidiyo a kafafen sadarwa na wani matashi da ya raba ƙafa s kan wani labari ya an ta surfa ashariya a waya, ya na kuma dauka a bidiyo.

Sai dai kuma tuni Abdullahi Ƴar-dubu ya shiga hannun ƴan sandan Caji-ofis ɗin Sharada, inda yanzu haka an tusa keyar sa zuwa shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama matashin, inda ya ce, tuni Mukaddashin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Abubakar Zubairu ya bawa DPO na Sharada, SP Abdulrahim Adamu umarnin a kamo wannan matashi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka an kamoshi kuma an mikashi babbar shelkwatar rundunar yan sanda da ke bompai.

SP Kiyawa ya ce nan gaba kaɗan za a sanar wa da al’umma halin da a ke ciki.

Tuni dai al’umma su ka fara shi wa rundunar ƴan sandan albarka bisa tashi tsaye da ya ta kamo wannan matashin cikin ƙanƙanin lokaci, inda kuma su ka riƙa yi masa tofin alla-tsine.

Ga Bidiyon Ku Kalla👇👇👇

https://youtu.be/7Lzj7IcOeC8

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button