News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un Tsawa Ta Fadowa Wata Yarinya A Makarantar Islamiyya A Jihar Jigawa

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un Tsawa Ta Fadowa Wata Yarinya A Makarantar Islamiyya A JiharJigawa

Kamar Yadda Muka Samu Rahoto Daga Wakilin Shafin Jaridar Rariya Hon Saleh Shehu Hadejia.

Inda Ya Wallafa Sanarwar Rasuwar Wannan Yarinyar Wadda Dalibar Makaranta Ce Kamar Haka.

Yanzu-yanzu wata tsawa mai karfi ta fadowa wata yarinya mai suna Maryam Rabiu Garba Kaugama a garin Kaugama dake jihar Jigawa.

Marigayiyar ‘ya ce ga tsohon dan majalistar taraiyya mai wakiltar Malammadiri da Kaugama.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ta je cikin makarantar Islamiyya domin yin karatun Alqur’ani Mai Girma.

Tabbas Wannan Yarinya Ta Samu Kyakkyawar Shahada, Wanda Ta Rasu Ne Akan Hanyar Zuwa Makaranta.

Anan Muke Addu’ar Ubangiji Allah Ya Jikanta Da Rahama Ya Gafarta Mata, Ya Bawa Iyayenta Hakurim Jure Wannan Rashi.

Allah Ubangiji ya gafarta mata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button