News

YANZU-YANZU: Tsawa Ta Yi Silar Mutuwar Dan Agaji Addinin Musulunci A Jihar Katsina

YANZU-YANZU: Tsawa Ta Yi Silar Mutuwar Dan Agaji Addinin Musulunci A Jihar Katsina

Rahotannin Da Muke Samu Yanzu-yanzu daga Nura Rabe Dandagoro jahar katsina na cewa.

Allah yayiwa wani dan Agaji a addinin musulimci rasuwa sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

 

Sakamakon ruwan da aka tafka hade da tsawa ta yi sanadiyyar rasuwar makwabcinmu mai suna Attahiru Abdu.

Wanda kafin rasuwarsa yana aikin Agaji a Addinin Muslimci na Fityanul Islam.

Marigayin yana zaune ne a garin Dandagoro dake karamar hukumar Batagarawa a jihar katsina.

Sannan ya rasu ya bar matarsa daya 1 da yaransa hudu 4 da iyayensa.

Allah ya gafarta masa Yasa Aljannah ce makomarsa, mukuma idan tamu tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani Amin.

Daga Nura Rabe Dandagoro

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button