News

BIDIYO: Bayani dalla-dalla kan yadda Abba Kyari ya shiga hannun NDLEA Kan Badakalar Hodar Ibilis

BIDIYO: Bayani dalla-dalla kan yadda Abba Kyari ya shiga hannun NDLEA Kan Badakalar Hodar Ibilis

Fassarar Dakta Furera Bagel

A ranar Juma’a 21 ga watan Janairu, 2022 ne, da ƙarfe 2 da minti 12 na rana, DCP Abba Kyari ya kira ɗaya da ga cikin jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA a garin Abuja.

Bayan minti biyu da kiran, sai shi jami’in ya mayar da kiran da ya yi masa. Sai Kyari ya ce masa zai zo wajensa bayan sallar Juma’a don su tattauna wata magana da ta shafi aiki.

Sai su ka haɗu a wajen da su ka shirya haduwar, kuma kai tsaye shi Abba Kyari ya fara bayani da cewa, yaransa sun kama wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da su ka shigo ƙasar nan da ga Ethiopia ɗauke da hodar Ibilis mai nauyin Kilogiram 25.

Abinda yake so shi ne, shi da yaransa zasu ɗauki kilo 15, su bar kilo 10 wanda da su ne za’a yi amfani wajen gurfanar da waɗannan masu safara a kotu a Enugu, inda a ka kama su.

Sannan kuma kilo 15 da Kyari da yaransa zasu ɗauka, sai a maye gurbinsu da hodar boge ta daidai yawan kilo 15 ɗin da ya ɗauka, yanda ba za a gane ba.

Abin da ya ke so da wannan jami’in na NDLEA shi ne ya taimaka wajen shawo kan manyansa na ofishinsu da ke Abuja, da su yarda da wannan shiri nasa.

Da ƙarfe 11:05 na safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, bayan hukumar ta bashi izininin nuna wa Abba Kyari cewa sun yarda da shirinsa, sai jami’in da Kyari ɗin su ka ci gaba da yin wayar bidiyo ta WhatsApp a gaba ɗaya wannan rana, inda ya faɗa masa cewa an yarda su ci gaba da wannan harƙalla.

Daga nan ne Abba Kyari ya faɗa masa cewa har sun raba kilo 15 ɗin da ya ɗauka shi da masu kawo bayanai (informants), waɗanda da su suka kawo masu labarin waɗannan masu safara. Inda su ka baiwa informants ɗin kilo 7 shi kuma da yaransa sun ɗauki kilo 8, har ma sun sayar da nasu kason.

Da ga nan ne sai ya ce ya na so shi ma wannan jami’in da mutanensa na hukumar, reshen Abuja su ci moriyar wannan harƙalla, inda ya ce in sun yarda zai sayar da 5kg daga cikin wancan kilo 10 da ya rage ya kawo masu kudin. Sai ya rage 5kg kawai na zallar hodar Ibilis da za a kai kotu sauran kuma a sa na boge.

Tun da a na sayar da kowane kilo na hodar ibilis ɗin kan Naira Milliyan 7, to kuɗin da zai kawo masu akan wannan kilo 5 ɗin zai zama naira miliyan 35, kenan. A dalar Amurka kuma ya kama $61,400 kenan.

Da ga nan ya matsa wa jami’in cewa ya kamata ofishin ma su na Abuja su karɓi su waɗanda a ke tuhuma da kuma sauran hodar Ibilis ɗin da ga hannunsu tunda suna nan a Abuja. Shi kuma ya ce yana wayar ne daga Legas inda yaje wata harka ta kansa.

Washegari, a ranar 25 ga Janairu, Abba Kyari ya ce zai turo ƙaninsa da ya kawo wa jami’in kuɗin, yaransa kuma su kawo masu laifin tunda baya nan, sai jami’in ya ce a’a ya fi so ya haɗu da shi ba wai ɗan aike ba.

A wannan rana, da misalin ƙarfe 5:23 na yamma, bayan Kyari ya dawo, sai su ka haɗu a wajen da su ka fara haɗuwa.

A cikin tattaunawarsu, Kyari ya faɗa wa jami’in na MDLEA yadda su ka sami labarin miyagun da ga wajen wani ‘informant’, wanda ya ke tare da gungun ‘yan safarar, kuma ya na tare da shi Abba Kyarin. Da ga nan ne yaransa su ka tashi zuwa Enugu su ka kama waɗancan.

Ya kuma ce a bisa umarninsa ne nan take su ka cire kilo 15 ɗin su ka maye gurbinsu da na boge, kuma su ka yi shaida a jikin mazubin na gasken yadda in an zo gwaji za a gane su.

Ya faɗa masa yadda in an kawo hodar Ibilis din NDLEA za a gane kilo 5 din da su ka rage, wanda su ne asalin hodar, za a gansu da ɗigon launin ja sabo da kar a zo yin gwaji don hakikancewa ita ce, kuma a ɗauko ta boge.

Ya kuma tura wa jami’in hoton fakitin kilo 5 ɗin da ya rage yadda za su gane. Da ga nan sai a ka kuma shirya cewa kilo 5 shi kadai za a ɗauka a gwada, tunda a na ganin hodar ce ta gaske, ba sai an taɓa sauran na bogin ba.

Kyri ya kuma kawo kudin wadancan kilo 5 da su ka sayar a madadin NDLEA, wato dala 61,400 amma jami’in ya ce ba zai karba a waje ba sai a cikin mota.

Da ga nan ne su ka shiga mota, wacce an riga an sa na’urar ɗaukan magana da na bidiyo, inda a ke jin sa ya na bayani da bakinsa a kan harkallar.

https://youtu.be/xQaDQFdTPT0

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button