News

BIDIYO: Bazamu Lamunci Kisan Da Akewa Yan Arewa A Kudancin Nigeria Ba, Kodai Gwamnati Ta Dau Mataki Tun Kan Lokaci Ya Kure Mata

BIDIYO: Bazamu Lamunci Kisan Da Akewa Yan Arewa A Kudancin Nigeria Ba, Kodai Gwamnati Ta Dau Mataki Tun Kan Lokaci Ya Kure Mata

Gamayyar Kungiyoyin Farar-Hula a Arewacin Najeriya sun ja hankalin Shugabannin Arewaci da na Kudanci da kuma gwamnatin tarayya, da su dauki matakin kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa ‘yan asalin Arewacin kasar da ke harkokinsu a Kudu Maso Gabashin kasar kafin lokaci ya kure.

Wannan na zuwa bayan da a farkon mako wasu ‘yan bindiga suka kashe wata mata mai suna Harira da ‘ya’yanta hudu da kuma wasu yan Arewacin kasar da ke sana’o’i a jihar Anambra.

Mijin matar kuma mahaifin ƴaƴan dukkaninsu mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴaƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

Na shiga tashin hankali, saura kaɗan na haukace – kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji,” in ji Jibril Ahmed,

Yanzu ina zan fara – yaya zan yi aure har na samu ƴaƴan da Allah ya ba ni waɗanda har sun yi nisa da karatu.”

“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ɓarnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” in ji shi.

Bayan haka kuma maharan sun kona tirelolin dakon kaya da rahotanni basu ce ga adadinsu ba duk dai a jihar ta Anambra.

Amma yanzu tun da suke kashe mutanen nan baka ji wani babba a Arewa ya fito ya fito ya yi magana ba.

Amma da Arewa ne wani abu ya faru da yanzu ka ji sun fito sun fara magana suna cewa an dau doka a hannu,” in ji Nastura Ashir Shariff.

A kan haka kungiyar ke ganin mafita daya ce, wato a kyale mutanen Kudancin kasar su balle daga kasar kamar yadda suke bukata, don a cewar shugaban na CNG babu wata gwamnati da za a kafa a gabar da ake ciki da za ta iya magance wannan matsala.

Kisan Harira da ya’yanta hudu mata a jihar Anambra da ake zargin kungiyar IPOB da aikatawa ya fusata yan Arewacin Najeriya.

Lamarin ya janyo tada jijiyar wuya a shafukan sada zumunta, inda da dama ke sukar gazawar gwamnati, da kuma yadda Shugabannin Arewacin kasar da sauran masu fada a ji suka yi gum da bakinsu, kamar ba su san me ya faru ba a cewar wasu masu amfani da shafukan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button