News

BIDIYO: Yadda Akai Jana’izar Harira Da Yaranta Hudu Wadanda Duk Suka Gamu Da Ajalinsu A Hannun Yan Kungiyar IPOB A Jahar Anambra.

BIDIYO: Yadda Akai Jana’izar Harira Da Yaranta Hudu Wadanda Duk Suka Gamu Da Ajalinsu A Hannun Yan Kungiyar IPOB A Jahar Anambra.

“Mun yanke shawarar binne su a Awka ranar Laraba (yau), saboda jami’an dakin ajiyar gawa ba su ba su kulawa da ta dace ba, ba su sanya musu sunadaran adana ba.

“Shi ya sa ba za mu iya tafiya da su ba, domin sun riga sun fara rubewa, yanzu ba mu da wani zabi sai mu binne su a nan Awka,” inji basaraken.

Ya bayyaan haka ne a lokacin da yake bayani kan dalilinsu na jingine shirin kai gawarwakin zuwa mahaifarsu a Jihar Adamawa, domin yi musu jana’iza.

Yanzu ba ni da kowa —Malam Jibril
Tun da farko, magidancin da haramtacciyar kungiyar IPOB ta yi wa iyalan nasa wannan kisan gilla, Jibril Ahmed, ya ce yana cikin matukar tashin hankali kuma kungiyar ta shafe iyalansa gaba daya daga ban kasa.

“Yanzu babu wanda ya rage min, sun shafe daukacin iyalina; Ina cikin tsanain tashin hankali, ya kamata gwamnati ta kawo min dauki, ta dauki mataki” inji Jibril, wanda ke aikin gadi a wani gida a Jihar Anambra.

Malam Jibril, ya ce an yi wa iyalan nasa wannan gisan kiyashi ne a cikin makon da suke sa ran matar tasa, marigayiya Harira za ta haihu.

Magidancin ya yi zargin cewa an kashe Harira da ’ya’yansu hudu ne saboda an gan su sanye da hijabi a lokacin da suke dawowa daga ziyarar da suka kai wa kanwarsa.

Ya ce iyalan nasa da aka kashe sun hada da matarsa Harira Jibril mai shekara 32, sai ’ya’yansu hudu; Fatima mai shekara tara; Khadijah mais hekara bakwai; Aziza mai shekara biyar; sa kuma ’yar autar, Zaituna mai shekara biyu.

A zantawarsu da wakilinmu ta waya a ranar Tatala, Jibril ya ce, “Yanzu haka ina kokarin karbar gwarwakin ne; ’yan sanda sun ba ni takardun da zan je in karbi gawarwakin.

“Yanzu haka ina dakin ajiyar gawa, sun ce sai na biya N30,000 karin su samar min gawarwakin iyalina.

“Ina so in tafi da gawarwakin a binne su a Karamar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa, saboda makabartar da ke nan ta cika.”

Daga baya ne suka sauya shawarar binne mamatan a garin Akwa na Jihar ta Anambra.

Ga Bidiyon


Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button