News

BIDIYO: Bidiyon Katafaren Sabon Kamfanin Sarrafa Taki Da Dangote Ya Bude Na Dala Biliyan 2.5

Bidiyon Katafaren Sabon Kamfanin Sarrafa Taki Da Dangote Ya Bude Na Dala Biliyan 2.5

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce rukunin Dangote ne na biyu wajen daukar ma’aikata a Najeriya, bayan gwamnatin tarayya.

Ya fadi haka ne a Legas, lokacin da ya kaddamar da kamfanin takin zamani na Dangote wanda aka gina a kan dala biliyan 2.5, mai karfin tan miliyan uku. Kamfanin wanda ke Ibeju Lekki an gina shi ne akan fili mai fadin hekta 500.

Da yake jawabi a wajen taron, Buhari ya bayyana cewa tuni kamfanin takin ya fara fitar da kayayyakinsa zuwa wasu kasashe da suka hada da Amurka da Mexico da Indiya da kuma Brazil.

Shugaban ya kara da cewa gudunmawar da masana’antun Dangote ke bayarwa ya kara tabbatar da shugabancin Najeriya a nahiyar Afirka.

A jawabinsa na maraba, shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa, kamfanin da ake kaddamarwa shine kamfanin granulated urea mafi girma a Afirka, kuma na biyu mafi girma a duniya.

https://youtu.be/LMAF2aKsZ-w

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button