Uncategorized

BIDIYO: Daga Karshe Dai Jaruma Hadiza Gabon Tayi Cikakken Bayani Game Da Soyayyar Ta Da Mutumin Da Yakaita Kotu Akan Taqi Aurensa

BIDIYO: Daga Karshe Dai Jaruma Hadiza Gabon Tayi Cikakken Bayani Game Da Soyayyar Ta Da Mutumin Da Yakaita Kotu Akan Taqi Aurensa

Shahararriyar Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta cewa ta san wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa mai shekaru 48 da haihuwa, wanda ya yi ikirarin cewa ta yi alkawarin aurensa bayan ya kashe mata N396,000.

Jarumar wadda ta bayyana a gaban kotun shari’ar musulunci a ranar Talata, a Magajin Gari Kaduna, ta shaida wa kotun cewa ba ta taba sanin mutumin da ake magana ba, kuma ba ta da wata alaka da shi.

A makon da ya gabata ne mutumin ya shaida wa kotu cewa jarumar ta yi alkawarin aurensa, inda ya ce kawo yanzu ya kashe mata Naira 396,000.

Amma da take magana ta bakin lauyanta Barista Mubarak Sani Jibril a harabar kotun, Gabon ta musanta zargin da ake mata.

“Bayan jin zarge-zargen nasa, a zahiri ta bayar da nata martanin wanda ba shakka a cewarta, ba ta taba haduwa da shi ba, ba ta taba sanin abin da ya faru ba. Ya hadu da ita a Facebook wanda ya ce mallakarta ne, don haka, ba mu san komai ba game da hakan; mun saurare shi, za mu bar kotu ta yanke hukunci,” inji Mubarak.

Shima lauyan wanda ya shigar da karar, Barista N. Murtala, ya ce wanda ake kyautata zaton masoyin wanda ya kasance wanda yake karewa ne ya hadu da jaruma Gabon a Facebook, inda daga nan ne suka yi abota, inda ya kara da cewa ta yi alkawarin za ta aure shi kuma ya fara kashe mata kudi.

“Sun hadu a Facebook, daga nan ne suka yi abota, kuma matar ta yi alkawarin aure shi kuma ya fara kashe mata kudi. Ta musanta cewa ba ta san shi ba, amma mun sanar da kotu cewa za mu kawo shaidu kan hakan,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa ba su adawa da ba da belin ta saboda laifin da ake iya bayar da beli ne.

Alkalin kotun, Khadi Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Yunin 2022 tare da bayar da belin ta da sharadin bayar da mutane biyu da ke zaune a jihar.

Rahoton Fadeelah Omar Abdulmalik

#jaridaradio 14/6/2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button