News

BIDIYO: Gagarumar Nasarar Da Sojojin Nigeria Suka Samu A Sansa nonin Bello Turji Da Na Ragowar Yan Bindigar Daji

BIDIYO: Gagarumar Nasar Da Sojojin Nigeria Suka Samu A Sansanonin Bello Turji Da Na Ragowar Yan Bindigar Daji

ZAMFARA: Sojojin Sama Na Ci Gaba Da Kai Farmaki Kan Sansanonin ‘Yan Bindiga.

Jiragen yakin sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin hatsabinin dan bindigar nan Bello Turji su ka kashe mutanensa da dama.

Jiragen yakin kazalika sun kuma kara yin dirar mikiya akan karin wasu sansanonin yaran Bello Turji a gabashin Shinkafi a yankin  da ya hada da Gambiro, Jena, Kalage, Tungan Nasarawa da Awala kuma ganau din yace nna samun nasara sosai.

Matsin lambar da sojojin saman ke yi wa yan bindigar ya sa su kuma barayin suka dau matakin uzzurawa matafiya amma dakarun sun yi maganinsu.

Hanyar Shinkafi ita ce hanya mafi sauki wacce idan yan ta’adda sun tare hankalin kowa ke tashi saboda ita ce hanya da ta isa har Gusau babban Birnin jihar.

Wannan hanya kazalika ita ce dai zata je Kauran Namoda, Zurmi ko Talatan Maifara daga Shinkafi ko in an fito daga Isa ko Sabon Birni a jihar Sokoto.

Yan bindigar sun mamaye hanyoyin inda jami’anta tsaro su ka yi ta fatattakar  su, koda yake daga bisani can wajajen la’asar barayin sun yi awon gaba da wasu matafiya mota uku kafin isowar jami’an tsaro.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

https://youtu.be/Bdrw0gskB6Y

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button