News

BIDIYO: Yadda Al’ummar Karamar Hukumar Mariga Ke Neman Gawarwaki Sama Da 500 Da Ambaliyar Ruwa Tayi Awon Gaba Dasu A Jahar Neja

BIDIYO: Yadda Al’ummar Karamar Hukumar Mariga Ke Neman Gawarwaki Sama Da 500 Da Ambaliyar Ruwa Tayi Awon Gaba Dasu A Jahar Neja

Innalillahi wa inna ilaihir raju’in Wani Rahoto da muke samu yanzu-yanzu daga jahar neja na cewa.

Al’ummar garin Mariga da ke karamar hukumar Bariga a jihar Neja da ke Najeriya na kan neman gawawwaki sama da 500, da ake fargabar ambaliya ta yi awon gaba da su daga wata makabarta da ke garin.

Babban limamin Mariga Alhaji Alhassan Na’ibi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga BBC Hausa a ranar Laraba.

”Ambaliyar ruwa ta lalata kaburbura fiye da 1500, amma an sake binne gawawwaki kimanin dubu daya”, in ji limamin.

Ya kara da cewa yanzu haka ana neman sama da gawa 500 da suke tunanin ambaliya ta yi gaba da su a makabartar Mariga.

To amma limamin ya ta’allaka matsalar da aikace-aikacen masu hakar ma’adanai a kusa da makabartar, don a cewarsa ba su taba fuskantar yanayi irin wannan ba a sama da shekaru 60.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button