Religion

BIDIYO: Bidiyon Yadda Pastor Ya Raba Alluna Ga Al’majirai A Wata Makarantar Allo A Jahar Kaduna

BIDIYO: Bidiyon Yadda Pastor Ya Raba Alluna Ga Al’majirai A Wata Makarantar Allo A Jahar Kaduna

A yayin da ake cigaba da bukin ranar zaman lafiya ta duniya a yau Laraba, Shugaban Kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya, Pastor Yohanna Buru ya kai tallafin kayan karatu a wasu makarantun Allo na jahar Kaduna don kyautata alaka tsakanin Musulmi da Kirista.

Ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara dai ita ce ranar zaman lafiya ta duniya kuma a jahar Kaduna, malaman addinin Kirista da Musulmi sun yi amfani da ranar wajen raba kyaututtukan kayan karatun allo a wasu makarantu.

Malam Lawal Muduru na cikin ‘yan-tawagar Pastor Yohanna Buru kuma ya ce aikin da kungiyar wanzar da zaman lafiyan ke yi na kara kyautata alaka tsakanin Kirista da Musulmi.

Daya daga cikin Malam makarantun allon da aka kaiwa allunan rubutu da dawada, ya ce lallai zumunci ya kullu.

A baya can dai jahar Kaduna na cikin Jihohin da aka yi ta samun rikicin Kabilanci da addini, sai dai ire-iren wadannan tarurruka sun kara wayar da kan al’uma da sauran mabiya ta yadda yanzu ake zaune lafiya da juna.

Saurari rahoton cikin sauti:

https://youtu.be/gw3oKh7NKkc

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button