News

BIDIYO: Gaskiya Ta Fara Yin Halinta Angano Wani Abu Da NDLEA Take Boyewa Yan Nigeria Kan Abba Kyari

BIDIYO: Gaskiya Ta Fara Yin Halinta Angano Wani Abu Da NDLEA Ta Boyewa Yan Nigeria Kan Abba Kyari Daga Datti Assalafy

DAGA Datti Assalafiy

(1) Masu safarar hodar iblis (cocaine) da suka shigo dashi Nigeria daga Kasar Ethiopia suka sauka a filin jirgin saman Enugu su 13 ne, jami’an NDLEA maciya amana da suke aiki a fili jirgin sune maciya amana wandanda suke hulda da masu safaran miyagun kwayoyi ba Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari ba

(2) A cikin mutane 13 da suka shigo da hodar iblis Nigeria ‘yan sandan IRT sun samu nasaran kama mutane biyu ta dalilin ‘dan leken asiri mai bada bayanan sirri (Informant)

(3) Abinda ya shigo da DCP Abba Kyari cikin wannan lamari Wallahi taimako ne domin a biya Informant hakkinsa, saboda informant din yace bai yadda da kowa ba sai Sarkin Yaki

(4) Jami’in NDLEA da ya shiyarwa Sarkin Yaki bidiyon a cikin mota ba Musulmi bane, ya fito daga yankin Arewa maso gabas, lokacin bayyanashi baiyi ba saboda tsaro, Sarkin Yaki ya daukeshi tamkar dan uwa, amma saboda tsabagen cin amana da kiyayyar Musulunci ya hada baki da wakilan IPOB suka kitsa masa mummunan tuggu suka canza gaskiya domin a cutar da dan uwan mu

(5) An shigo da hodar iblis kimanin 25kg amma ace wai an wuce da hodar ba tare da jami’an NDLEA sun iya ganowa ba sai da ‘yan sanda suka kama?

(6) Maigirma Shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP Usman Baba Alkali yace hukumar NDLEA su binciki jami’ansu dake aiki a filin jirgin Enugu domin wadanda ake zargi masu safaran hodar iblis sunce suna aikin safaran hodar iblis tare da su domin akwai bidiyo da suka fadi haka a gaban ‘yan sanda, amma sai NDLEA take kokarin ta karesu saboda bata san cewa ‘yan sanda suna da bidiyo ba

(7) Inda nufin dakarun ‘yan sandan IRT cin amana ne, to tunda su suka kama masu safaran hodar iblis din ba zasu kaiwa NDLEA ba, da zasu karbi abinda suka karba ne su sallamesu ba wanda ya sani, ko kuma su bugesu a jeji shikenan an wuce layinsu sai a lahira, amma basuyi ba suka mika wa NDLEA

Gaskiya zatayi halinta, duk abinda zasu kitsa su tsara Wallahi NDLEA ba su isa su boye gaskiya ba akan wannan makircin da suka kulla

Muna jawo hankalin Gwamnatin Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ta kafa kwamitin bincike na musamman akan wannan zargi da makirci da aka kulla

Muna rokon Allah Ya tabbatar da gaskiya

https://youtu.be/5fM6aZm8BEM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button