News

BIDIYO: Gaskiyar Magana Kan Zarge Zargen Da Akewa Jami’in Yan Sanda Abba Kyari

Idan Baku Mantaba mun kawo muku wani rahoto kan cewa, Rundunar ƴan sandan Naajeriya ta ce ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyar tare da wasu ƴan sanda huɗu kan zargin ta’ammali da hodar iblis.

Harma cikin Rahoton Muka Kara Da Cewa, Wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin Litinin ta ce an kama mutanen ne bisa zargin hɗa kai wajen aikata miyagun laifuka, da saɓa ƙa’idar aiki.

Kuma Sanarwar na zuwa ne sa’o’i bayan hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce tana neman mataimakain ƴan sandan ruwa a jallo saboda zargin ta’ammmali da hodar iblis.

Kakakin rudunar DSP Olumuyiwa Adejobi yace an kama mutanen ne bayan wasu bayanai da hukumar ta NDLEA ta fitar.

Tuni aka damƙa Abba Kyari da saurna ƴan sandan da ake zargi ga hukumar NDLEA don gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi.

Sanarwar ƴan sanda ta ce tuni kuma aka fara shirin ladabtar da jami’an ƴan sandan da ake zargi a cikin gida.

Wasu kafofin watsa labaran ƙasar sun rawaito cewa yanzu haka ana tsare da Abba Kyari a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake Abuja.

Wane ne Abba Kyari?
Wadanne tuhume-tuhume ne a kansa?
Za a kai shi Amurka ko a Najeriya za a yi shari’arsa?

Ku Kalli Wannan Bidiyon Dan Samun Wadannan Amsoshin

https://youtu.be/QIxOxE-OsWw

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button