News

BIDIYO: Gwamna Matawalle Ya Baiwa Wani Babban Malamin Musulunci Gudummuwar Naira Miliyan 12, Domin Zuwa Kasar Saudiyya Neman Lafiya

BIDIYO: Gwamna Matawalle Ya Baiwa Wani Babban Malamin Musulunci Gudummuwar Naira Miliyan 12, Domin Zuwa Kasar Saudiyya Neman Lafiya

Daga Isah Abdullahi Dankane

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya bada gudummuwar naira miliyan goma sha biyu ga wani babban malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, mai suna Sheikh Malam Abdullahi Dalla-Dalla.

Gwamna Matawalle ya bada tallafin kudin ne domin Shehin Malamin ya tafi kasar Saudiyya wurin neman lafiya.

Sheikh Abdullahi Dallla Dalla, ya dade kwance yana fama da jinya a asibitin Gwamnatin tarayya dake jihar ta Zamfara, wanda har yanzu bai samu lafiya ba.

Wanda shine likitocin dake kula da shi suka tabbatar masa da cewa dole sai ya tafi kasar Saudiyya a can ne suke da ingantattun kayan aikin da za su magance matsalar rashin lafiyar dake damunsa.

Nan take Gwamnan jihar ya bayar da umurnin a gaggauta ba shi gudunmuwar wannan kudi.

Anan Muke Addu’ar Ubangiji Allah Ya Bashi Lafiya Yakuma Dawo Dashi Gida Lafiya Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button