Kannywood News

BIDIYO: Har Naira Dubu Hamsin Na Biya Ladin Cima A Fim Din Gidan Badamasi, Cewar Nazir Adam Salih

Har Naira Dubu Hamsin Na Biya Ladin Cima A Fim Din Gidan Badamasi, Cewar Nazir Adam Salih

Fitaccen marubuci a masana’antar Kannywood, Nazir Adam Salihi, ya karyatu batun da jaruma Ladin Cima ta yi cewa ba a taba biyan ta kudi masu kauri ba.

Bayan nasa na zuwa ne bayan wata tattaunawarta da BBC ta yi da Ladin Cima, inda take cewa ba a taba biyan ta N50,000 ko N30,000 ko N20,000 ba a fim; Hasali ma fim na karshe da ta je, N2,000 aka biya ta.

Da yake bayani, fitaccen marubicin ya ce, “Nazir: Na biya Ladi Cima (Tambaya) N4o,000 a fim din Gidan Badamasi Kashi na uku; na sake biyan ta N30,000 a kashi na hudu.

“Haka nan ko wata daya ba a yi ba na sake biyan ta N30,000 a wani dan bidiyo na fadakarwa kuma a duka ba ta yi fitowa sama da goma ba.

“Haka nan mun yi gyaran scene guda wanda magana kawai ta yi muka biya ta N5,000 muka kuma saya mata abinci na kusan N4,000 a wuni guda.

“Haka nan a gabana, Hadiza Gabon ta ba ta N270,000 kyauta! Amma duk da haka ka ji halin dan Adam. Kai jama’a!” inji shi kamar yadda ya rubuta a Facebook.

Aminiya ta kira marubucin, inda ya tabbatar da cewa shi ya yi rubutun, sannan ya kara da cewa ya yi rubutun ne domin ya fayyace batun da ta yi na cewa ba a biyan ta da kyau a fim.

Ladin Cima ta tayar da kura ne bayan ta bayyana a tattaunawarta da BBC cewa ba a taba biyan ta N50,000 ko 30,000 ko 20,000 ba a fim, inda a ciki ta ce fim na karshe da ta je ma dubu 2 aka biya ta

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button