News

HANEEFA: Me Ya Sa Masu Mulki Ba Sa Tururuwar Zuwa Ta’aziyya Ga Iyalan Wadanda ‘Yan Bindiga Ke Kashewa A Jihohin Katsina, Sokoto Da Zamfara

HANEEFA: Me Ya Sa Masu Mulki Ba Sa Tururuwar Zuwa Ta’aziyya Ga Iyalan Wadanda ‘Yan Bindiga Ke Kashewa A Jihohin Katsina, Sokoto Da Zamfara?

Daga Isyaka Laminu Badamasi

Wasu mutane na ta mamakin yadda masu mulki ke ta tururuwar zuwa ta’aziyya wa iyayen Hanifa da aka kashe a jihar Kano, amma ba su yin tururuwar zuwa ta’aziyya wa al’ummar Sabon Birni na jihar Sokoto da aka Kona su da ran su, ko jama’ar jihar Borno, Yobe, Adamawa, Zamfara ,Katsina da Kaduna da kullum ke cikin zullumi ba?

Kisan Hanifa kowa ya amince da an yi, amma duk kashe rayukan mutane da lalata dukiyar al’umma da ake yi a wadannan jihohi mutane ba su yarda ana yi ba, hasali ma kiran wadanda suka nemi a dauki mataki kan haka mutane ke yi da makiya Kasa, marasa kishi, makiya Buhari da jam’iyyar APC; wata kila su ma masu mulkin ba su yarda ana kashe kowa ba ne shi ya sa ba su zuwa, idan kuma suka je harkar siyasar su ba su ce uffan Kan batun jajantawa.

Ba ku ga yadda mutanen Sokoto da Borno suka taryi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ne? Shin idan da sun yarda ana kashe su kuma gwamnati ba ta dauki mataki ba za su fito su tarye shi haka?

Ba wani Dan siyasar da zai kawo muku ziyarar jaje har sai kun yarda ana kashe ku, to idan suka kawo muku ziyarar jaje kuma su ne jami’an gwamnati, to ai sun amince sun gaza Kenan.

-Rariya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button