Kannywood News

CIKIN BIDIYO: Jarumin Kannywood Ali Nuhu Tare Da Jarumi Kuma Mai Bada Umarni Falalu A Dorayi Sun Mayarwa Da Ladin Cima Martani.

Jarumin Kannywood Ali Nuhu Tare Da Jarumi Kuma Mai Bada Umarni Falalu A Dorayi Sun Mayarwa Da Ladin Cima Martani.

Jarumi kuma mai shirya fina-finai a Kannywood Ali Nuhu ya tofa albarkacin bakinsa kan ikrarin da ‘yar wasa Ladin Cima ta yi inda ta ce ana biyanta Naira 2,000 zuwa 5,000 bayan yin fim.

Jarumin Ya Bayyana cewa ko a aikin da mukai da ita mun bata naira dubu 40.000 a cewar sa.

Yayinda shima mai shiryawa dakuma bada umarni wato falalu a dorayi yake cewa.

Falalu A Dorayi wanda ke shirya fina-finai a Kannywood ya musanta kalaman ‘yar wasa Ladin Cima inda ta ce ana biyanta naira dubu biyu zuwa dubu biyar a duk lokacin da ta yi fim.

Falalu a dorayi cewa yayo shima. Ban taba bawa ladin cima lasa da dubu Ashirin ba A Cewar sa.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Instagram na ta ce-ce-ku-ce kan wasu kalamai da ɗaya daga cikin ƴan wasan Kannywood ta yi na cewa ana biyanta naira dubu biyu zuwa dubu biyar a duk lokacin da ta yi fim.

A hirar da BBC Hausa ta yi da ita a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita, Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ta kasa mallakar muhalli shi ne tun daga lokacin da ta soma wasan kwaikwayo a zamanin mulkin Yakubu Gowon, ba ta taɓa samun kuɗi a dunƙule dubu ashirin ko talatin ko hamsin idan ta yi fim ba.

Wannan batu nata ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta inda jama’a ke ta zargin daraktoci da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar cewa ba su kyautata wa ƴan wasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button