News

BIDIYO: Kiyiwa Allah Ki Saki Danmu Da Aka Riqa Jibga A Gabanki Kina Kallo- Iyayen Aminu Ga Aisha Buhari

BIDIYO: Kiyiwa Allah Ki Saki Danmu Da Aka Riqa Jibga A Gabanki Kina Kallo- Iyayen Aminu Ga Aisha Buhari

Muna rokonki Aisha Buhari, ki wa Allah ki sa a saki ɗan mu Aminu da aka kama – Rokon Iyayen Aminu ga Aisha Buhari

Iyayen matashin nan mai suna Aminu Azare da Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta sa aka kama sun mika kokon barar su da rokon Aisha Buhari ta yi wa ɗan su sassauci ta sa a sake sa bayan ta sa a kama shi.

Idan ba a manta ba Aisha Buhari ta aika dakarun rundunar tsaron SSS zuwa har garin Dutse inda suka fantasama Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse, suka kama Aminu Azare, matashi da yake mataki na uku.

Ana tuhumar Aminu ne da laifin cin mutuncin uwargidan shugaban kasa ta hanyar wani rubutu da yayi ya saka hoton Aisha Buhari.

A rubutu Aminu Azare ya ce ‘ Su Aisha Buhari an ci kudin talakawa an yi ƙiba’.

Kawun wannan matashi ya bayyana wa BBC Hausa cewa ba su san lokacin da aka tafi da Aminu ba sai daga baya da SSS suka bashi waya ya kira mu cewa yana Abuja an kama shi bisa rubutun da yayi da ya saka a shafin sa tun watan Yuni.

Wannan rubutu bai yi tasiri ba sai a watan Nuwamba.

” Jami’an tsaron SSS sun tasa keyar Aminu har fadar shugaban kasa, gaban Aisha Buhari inda suka rika jibgarsa a gabanta, ya na kuka, tana zaune ta na kallo.

” Mu dai rokon mu shine a tausaya wa Aminu ta yafe masa a sake shi.

Suma hukumomin jami’ar da yake karatu sun ce basu san lokacin da SSS suka dira jami’ar ba suka waske da Aminu.

Ƴan Najeriya da dama da suka tofa Albarkacin bakin su akai sun yi tir da abinda Aisha Buhari ta yi wa wannan matashi, suna mai cewa tana gwamnati ay dole a rika mata haka da koma waye.

” Da ace ɗan kudu ne ya faɗi haka babu wanda ya isa ya kama shi amma da yake ɗan Arewa ne bashi da gata, sai ma cewa ake yi Allah Kara. Wani irin abu ne ba ayi wa Patience Jonathan ba, har zane an rika yi nata. Bamu taba jin an ce wai ta sa akama wani ba.

 

” Lokaci ne, wata rana sai labari. Kwana nawa ne ya rage, ga mai rai saura ne. Fatan mu dai Allah ya fiddo da shi lafiya” in ji wani mazaunin Kano Saminu Hamza.

Kakakin uwargidan shugaban kasa, Aliyu Abdullahi ya ki yin bayani game da abin, da ga jin kirar daga wakilin PREMIUM TIMES ne sai ya yi maza maza ya ce ” Ina mitin, Ina mitin”

https://youtu.be/Je5RiPV-rUA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button