News

BIDIYO: Mahaifiyata Nake Son Taimako Cewar Wani Yaro Mai Kuka Yana Aikin Birkilanci

BIDIYO: Mahaifiyata Nake Son Taimako Cewar Wani Yaro Mai Kuka Yana Aikin Birkilanci

“Mahaifiyata nake son taimako” Cewar yaro mai kuka yana aikin birkilanci

Bidiyon wani yaro mai aikin ƙwadago na birkilanci ya sosa zuciyar mutane da dama.

A cikin bidiyon an nuna yaron yana a wajen aikin birkilanci yana aiki yana kuka.

Bayan bidiyon sa na farko ya karaɗe yanar gizo, wanda ya wallafa bidiyon mai suna Lukman Samsudeen, ya bayyana wasu abubuwan ban tausayi dangane da yaron mai suna Kamarudeen. Jaridar Yen.com.gh ta rahoto.

An bayyana wasu abubuwa game da rayuwar yaron.

A wani sabon bidiyo da ya saka a TikTok, Lukman yace yaron yana zaune tare da shi kuma mahaifin sa ya rasu, yanzu haka maraya ne.

Lukman yace Kamorudeen yana aikin ne domin ya ga ya taimakawa mahaifiyar sa wacce manomiya ce.

Lukman, yaron yana ganin mahaifiyar sa sai ɗaya kawai a shekara cikin watan Disamba. Ya nemi mutane da su taimaki yaron, inda ya ƙara da cewa yaron yana son zuwa makaranta.

Kalli bidiyon a nan

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button