News

BIDIYO: Matar Abdulmalik Tanko Tace Tana Neman Mijin Ta Ya Sake Ta Saboda Bazata Iya Zaman Jiran Sa Ba

Hanifa: Ina neman miji na ya sake ni dan ba zan iya zaman jira ba — Matar Abdulmalik Tanko

Jamila Muhammad Sani, matar Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar a Jihar Kano, ta ce ta na son mijin nata ya rubuta mata takardar saki.

A jiya Juma’a ne dai a ka gurfanar da Jamila, mai shekara 30 da haihuwa a Kotun Majistare 12 da ke zamanta a Gidan Murtala, bisa zargin haɗin baki da ita a ɓoye marigayiya Hanifa.

Gurfanar da Jamila ɗin ya zo ne bayan da a ranar Alhamis ta baiyana a gaban Babbar Kotun Jiha 5, a bisa jagorancin Mai Shari’a Usman Na-abba, ta bada shaida a kan yadda Tanko ya kawo Hanifa gidansa har ma ya yi ƙaryar cewa mahaifiyar yarinyar ce ta yi tafiya zuwa Abuja.

Sai dai kuma da a ka gurfanar da Jamila a gaban kotun, alƙalin kotun, Muhammad Jibril, ya wanke ta ya kuma umarci da a sake ta da ga inda a ke tsare da ita tun lokacin da a ka kama mijin nata.

Da ta ke zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, Jamila ta gode wa Allah bisa wanke ta da Ya yi kuma ta ji daɗi a bisa hukuncin na kotu.

A cewar ta, ita yanzu ta ne neman Tanko ya sake ta sabo da ba za ta iya zaman dakon jiran sa ya fito ba.

“Ni da har yanzu da ƙuruciya ta. Ba zan iya zaman jiran sa ba. Ni kawai ina neman ya sake ni in je in samu wani mijin na aura. Ni ba zan iya zaman dako ba,” in ji Jamila.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button