Religion

Full Abinda Daurawa Ke Nufi Da Mafi Munun Mace Shine Gaban Ta -Inji Sheikh Daurawa.

MAFI MUNI A JIKIN MACE SHI NE GABANTA.
-Inji Sheikh Daurawa.

✍️ Mustapha Muhammad Rajab

Na kalli wani bidiyo na Sheikh Daurawa inda yake cewa an ce mace ce daɗin Duniya. shi ne yake tambaya to meye macen? mafi muni a jikin mace shi ne gabanta. nan take fitsari nan take fitar da jini. to meye na burgewa. shi ne shiyasa aka ɓoyeshi ai.
-Inji Sheikh Daurawa.

Da farko da na kalli bidiyo sai nayi masa uzuri hala yana magana ne da irin mutanen banza nan. sai kuma daga baya na gane su wanene ke cewa mace daɗin Duniya ce. A gaskiya Malam bai kyauta ba ya kamata ya fito Midiya yabawa ƴaƴa mata na duniya gaba ki ɗaya Haƙuri akan wannan katoɓara da ya tafka.

Wannan wajen da yake magana shi ne mafi daraja a jikin ƴa mace Idan ya tsira komai ya tsira daga jikin ƴa mace, idan ya ɓaci komai ya ɓaci daga jikin ƴa mace. Fitsari ko jini da yace yana fita daga wajen wannan wani lamari ne da Ubangijin mu ya tsara shi a hakan, wani irin shi ba zai iya munanta hakan ba.

Saboda darajar wajen ne ma ba ya halatta ga ɗa Namiji sai yayi Gwagwarmayar fitar hayyaci. Mutanen banza ke saɓawa Allah ta hanyar Fyaɗe ko zina don samun shi a hanya mafi muni. Ta wannan wajen da ka kira mafi muni tanan aka haifeka har yau kazo gaban mutanen da suke maka kallon mai daraja kake munanta shi. kowa yana samun daraja ne ta Asalin shi, wannan wajen shi ne Asalin ka Malam Daurawa. Ya kamata a dinga kiyaye harshe ba komai bane abin furtawa.

Dalilin da yasa aka ɓoye shi kuma ba saboda muninshi bane, abu mai daraja sanin kanka ne kulle shi akeyi a ɓoye. Akramakallah nawa ne a akawunt ɗin ka na banki? To ka fito dashi mana kana yawo dasu kaji yadda lamarin yadda zai canja. To amma meyasa ka ɓoye kuɗaɗen ka a banki baka bar su ba Uryanan.

Akramakallah wannan tunanin naka irin na mutanen zamanin Jahiliyya ne wanda basu ɗauki ƴa mace a matsayin komai ba, sai ƙasƙantacciya wulaƙantacciya wacce bata da wani daraja. Amfaninta kawai shi ne gabanta. to ka lura ma ko a lokacin ma ana yiwa ƴa mace kallon mai amfanin ta wajen da ka munanta. Kuma daman ba kowane Bahaushen arewa bane yake girmama ƴa mace.

Ba na son kawo maka Aya ko Hadisi Akramakallah Saboda kun fi mu ƙwarewa a wannan fagen amma dai ko ba komai duk wanda ya fahimci maganar ka da idon Basira yasan ka wulaƙanta ƴaƴa mata ne. kuma duk ɗan halas ba zai yi shiru ya kalle ka ba. saboda ko ba komai iyayenmu mata ne. muna da ƙanne mata. Yayyi mata. Malam a kiyaye harshe don Allah.

-Ustaz Aba Sajjadi Ra’isus Sunnah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button