Kannywood News

BIDIYO: Neman Afuwar Sheikh Ibrahim Daurawa Kan Kalaman Da Tayi Mai Wanda Suka Janyo Cece Kuce A Shafukan Sada Zumunta

Cikin Wani Yanayi Na Ban Tausayi, Jaruma Nafisa Ishak Wadda Taiwa Mallam Ibrahim Daurawa Martani Tafito Ta Nemi Afuwar Malamin.

Kamar Yadda Zaku Gani Cikin Wannan Bidiyon, Jarumar Tafara Ne Da Amsa Kuren Ta, Tare Da Rokon Afuwar Al’ummar Musulmi.

Sannan Ta Dora Faruwar Hakan A Matsayin Kaddara Daga Ubangiji Tare Da Cewa Babu Wanda Yafi Karfin Allah Ya Jarrabce Shi Haka.

Sannan Taja Hankalin Mutanen Da Idanuwan Su Kan Rufe A Lokacin Da Kaddararra Ta Zowa Wanin Su, Inda Tace Mai Makon Addu’a Sai Ayita Zagi Tare Da Mugun Fata.

Tace Tana Godiya Ga Masoya Yan Uwa Kawaye Da Abokai Da Sukai Ta Kiranta A Waya Suna Tambayar Lafiyar Ta.

Akwai Wadanda Ma Suka Ce Wai Ance An Kwa Kule Mata Idanuwa Wasuma Sukace An Kamata.

Tace Tana Nan A Gidan Su A Cikin Koshin Lafiya Kuma Tana Godiya Da Kulawa Da Zumunci.

Sannan Ta Kare Sakon Nata Da Cewa, Dafatan Mallam Zaiyi Mata Aikin Gafara Kuma Inssha Allahu Hakan Bazai Sake Faruwa Ba.

Gadai Bidiyon Nata Ku Kalla A Duk Inda Kuke.

https://youtu.be/nd0HaiKgmIs

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button