Kannywood News

BIDIYO: Rahama Sadau Na Shan Zagi Bayan Yin Wallafar Da Tai Na Ta’aziyyar Mutuwar Dan Davido Ifeanyi Adeleke

Fitacciyar Jarumar Kannywood Rahama Sadau na shan zagi bayan yin wallafar ta’aziyya ga Davido kan mutuwar ɗansa Ifeanyi Adeleke

Sanannen abu ne yadda jaruma Rahama Sadau tayi fice kuma take shan caccaka a kafafen sada zumuntar zamani wanda dama ba yau aka fara ba.

Jarumar ta saba yin wallafa iri-iri wadanda ke hassala mabiyanta har su dinga zaginta su na cin zarafinta da maganganu Marasa Dadi.

Akwai wadanda kan kira ta da marar kishin addini musamman ganin yadda take cudanya da mawaka da jarumai Wadanda Ma Ba Musulmai Ba A Matsayinta Na Ya Mace.

A wannan karon, jarumar ta yi wallafa ne tana yi wa mawaki Davido ta’aziyyar mutuwar dansa Ifeanyi Adeleke, wanda ya mutu a A Swimming Pool Din wanka ta shafinta na Twitter.

Duk da dai wasu na ganin ba matsala bace don musulma ta yi wa kirista gaisuwar Mutuwa.

Sai dai Wasu mutanen Na ganin akwai wadanda da dama su ka rasa ‘yan uwansu Batai Musu Ta’aziyya Ba, Harma akwai jaruman Kannywood, kamar su Nura Mustapha Waye da Kafi gwamna na Kwana Casa’in da su ka rasu kwanan nan kuma ba ta yi wallafa tana ta’aziyya ba.

Sai ga shi mawaki na kudu, ya rasa dansa ta fito duniya tana taya shi takaici.

Rubutun Wanda Jarumar Ta Wallafa Harma Ya Jawo Cece Kuce Ya fara ne da wallafar cewa:

“Zuciyata ta karye, ina yi wa Davido da Chioma ta’aziyyar rasa dansu da su ka yi. Ubangiji ka yafe mana.”

Bayan ganin idanu sun dawo kanta inda ake din caccakarta, ta kara da cewa dabbobi sun cika mata bangaren tsokaci, wasunsu ma magenta ta fi su. Anan ne ta sha zagi kala-kala daga mutane daban-daban.

Kukalli Bidiyon Anan 👇👇👇👇

https://youtu.be/YJZrfzX4NaE


 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button