Kannywood News

Bidiyo: Rahma Sadau tayi ƙorafi akan wadanda suka fassara fim ‘din Indiyan da ta fito a ciki.

Bidiyo: Rahma Sadau tayi ƙorafi akan wadanda suka fassara fim ‘din Indiyan da ta fito a ciki.

Fitacciyar jarumar Kannywood Rahma Sadau, tayi ƙorafi akan masu fassara fina-finan Indiya zuwa harshen Hausa a wannan lokaci.

Jarmar tayi korafin ne musamman ma ga wadanda suka fassara fim ‘din Khuda Hafiz wanda ta fito ta taka rawa a cikin sa a karo na farko.

Rahma dai itace jaruma ta farko a Kannywood da ta samu wannan gagarumar nasarar, ta fitowa a fim ‘din Indiya.

Domin kamar yanda jaruman Indiya suke da burin fitowa a fina-finan Hollywood na America, haka suma jaruman Kannywood suke da burin fitowa a fina-finan Indiya.


To tuni dai aka fassara fim ‘din na Khuda Hafiz da Hausa, sai dai Rahma tayi ƙorafi akai.

Kamar yadda zaku kalli bidiyon fassar fim din, dakuma korafin da jarumar tayi game da fassarar.

Jarumar dai tayi wannan korafi ne a shafukan ta na sada zumunta, inda dafari ta tambayi mai yasa ba’a bukaci tasa muryarta ba aciki.

Ga kuma labarin nan a ƙasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button