News

Innalillahi.. Bidiyon Yadda Aka Ciro Gawarwakin Wasu Mata Hudu Da Suka Gamu Da Ajalin Su A Ballewar Jirgin Ruwa A Jigawa

Innalillahi.. Bidiyon Yadda Aka Ciro Gawarwakin Wasu Mata Hudu Da Suka Gamu Da Ajalin Su A Ballewar Jirgin Ruwa A Jigawa

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wata yarinya ‘yar wata bakwai da wasu mata hudu bayan da kwale-kwalen su ta kife a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shi ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin jiya Talata, inda yarinyar da kuma matan suka shiga kwale-kwale daga Nguru a jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani na karamar hukumar Guri na jihar ta Jigawa.

“Abin takaici, kwale-kwalen ya kife suna daf da isa inda za su je. Amma matukin kwale-kwalen ya samu damar fita da ransa, yayin da su kuma fasinjojin suka nutse,” a cewar Shiisu.

Ya ce lokacin da lamarin ya faru, direbobi da ke yankin sun yi kokarin ceto fasinjojin abin bai yu ba, sai dai gano gawarwakinsu da aka yi.

DSP Lawan ya kara da cewa an kai gawarwakin zuwa cibiyar lafiya ta Adiyani kafin babban likitan asibitin ya tabbatar da mutuwarsu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce dukkan matan da lamarin ya rutsa da su ‘yan kauyen ne na Adiyani, inda ya kuma ce an fara bincike domin gano abin da ya janyo kifewar kwale-kwalen.

Karin Bayani 👇👇👇👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button