News

BIDIYO: Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Kama Fitacciyar Mai Barkwancin Nan Ta TikTok Murja Ibrahim Kunya.

BIDIYO: Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Kama Fitacciyar Mai Barkwancin Nan Ta TikTok Murja Ibrahim Kunya.

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu Yanzu Daga Jahar Kano Na Cewa, Rundunar Yan Sanda Jahar Ta Kama Murja Ibrahim Kunya.

Koda ya ke Ƴan sandan ba su yi ƙarin bayani ba, amma idan zaku iya tunawa a shekarar da ta gabata ne wani lauya ya shigar da ƙorafi inda yake neman da a binciki Murja da wasu fitattun mawaƙa da masu amfani da TikTok kan zargin ɓata tarbiyya.

An kama Murjar ne yayin da take tsaka da shirye-shiryen shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce, ta kama Murja Ibrahim Kunya bayan ƙorafin da Zauren Malaman Kano suka yi a kanta da wasu masu amfani da TikTok.

Wata majiya ta ƙara da cewa tuni manyan mutane suka shiga sahun neman a saki Murjan.

Zamu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani.

Ku Kalli Bidiyon Nan 👇👇👇👇👇👇👇

https://youtu.be/mXoXSCJUJ08

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button