News

BIDIYO: Sai Bello Turji Ya Ajiye Makamansa Sannan Za Mu San Da Gaske Yake Tuban Nasa – Shinkafi

BIDIYO: Sai Bello Turji Ya Ajiye Makamansa Sannan Za Mu San Da Gaske Yake Tuban Nasa – Shinkafi

A cewar Shinkafi, har yanzu matsayar da gwamnatin Zamfara ta dauka na janye batun yin sulhu da ‘yan fashin daji na nan daram, amma ya kara da cewa, duk wanda ya mika kansa, kofa a bude take.

Shugaban kwamitin da ke hukunta wadanda aka samu da laifukan ayyukan fashin daji da makamantansu a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce ba za su dauki tuban Bello Turji da muhimmanci ba, har sai ya ajiye makamansa da sauran kayayyakin da suke ta da zaune tsaye da su.

A karshen makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji, wanda fitaccen dan fashin daji ne da ya addabi wasu yankunan jihar Zamfara, ya tuba ya kuma rungumi zaman lafiya.

Turji da tawagarsa sun shahara wajen satar shanu, garkuwa da mutane da kai hare-hare akan kauyuka da ke yankunan kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a jihar ta Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriyar.

Sai dai yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC a ranar Litinin, Shinkafi ya ce akwai bukatar Turji ya ajiye makamansa, ya kuma fito bainar jama’a ya nuna cewa ya tuba idan har yana so gaskata shi.

“Gaskiyar magana ita ce, ya tuba, amma kuma har yanzu bai mika makamansa da wargaza tawagarsa ba.

“Idan har ka ce ka tuba, ya zama dole ka mika dukkan makamanka har ma da babura da kuke hawa da kayan soji da na ‘yan sanda da kuke sakawa.” In ji Shinkafi.

A cewar Shinkafi, har yanzu matsayar da gwamnatin Zamfara ta dauka na soke batun yin sulhu da ‘yan fashin dajin na nan daram.

Sai dai ya ce, duk dan bindigar da ya mika kansa da makamansa akan cewa ya tuba, gwamnati za ta karbe shi.

Shugaban kwamitin har ila yau ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun jinkiri wajen yin hukunci ga wadanda aka samu da laifi.

A shekarar 2019 da ya hau mulki, Gwamna Bello Matawalle ya ayyana shirin sulhu da ‘yan bindiga, a wani mataki na kawo karshen tashe-tashen hankulan da suka addabi jihar.

Sai dai a watan Satumbar bara, gwamnatin Zamfarar ta soke wannan shiri, bayan da ta zargi ‘yan bindigar da karya alkawuran da suka yi.

A baya bayan nan, hukumomi sun ba da umarnin mutane su nemi lasisi iznin mallakar bindiga a jihar ta Zamfara don su kare kansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button