Uncategorized

BIDIYO: Sarkin Hausawa Ya Karyata Yan Sanda Inda Yace An Kashe Hausawa A Ondo Da Nufin Ramuwar Gayya

BIDIYO: Sarkin Hausawa Ya Karyata Yan Sanda Inda Yace An Kashe Hausawa A Ondo Da Nufin Ramuwar Gayya.

Karya yan sanda suke mana cewar  Aka Kashe Mana, harin gayya aka kai mana a Ondo: Sarkin Hausawa.

 

Sarkin Hausawan Ondo ya karyata kwamishanan yan sanda jihar Ondo kan harin da aka kaiwa Hausawa,

A wani rahoto da ya fito a humanci cewa, An kashe mutum biyar a unguwar Hausawa dake jihar Ondo biyo bayan harin da aka kai Cocin Katolika Kakakin yan sanda jihar, SP Funmilayo Odunlami, tace ba hari aka kaiwa Hausawa ba, yan fashi ne.

Sai Dai Sarkin Hausawan Ondo, Alhaji Abdulsalam Yusuf, ya bayyana cewa harin da aka kai unguwar Hausawa a Ondo ba Sam Ba Yan fashi da makami bane kamar yadda yan sanda ke ikirari.

Alhaji Abdulsalam yace harin gayya aka kaiwa Hausawa da gayya kuma an kashe mutum biyar, Daily Trust ta ruwaito.

Akalla mutum hudu suka rasa rayukansu a harin da aka kai unguwar Sabo yayinda aka kashe mutum daya a unguwar Igba. Ya ce al’ummar Hausa/Fulani na zaman dar tun harin da wasu yan ta’adda suka kai cocin St Francis’ Catholic dake Owo.

Ya bayyana cewa:

“Muna watsi da jawabin yan sanda; karya ne cewa yan fashi ne. Babu abinda suka dauka, kawai hari suka kai unguwannin Hausawa biyu.” “Mutum hudu suka rasa rayukansu a unguwar Sabo dake Akure – mutum biyu Hausawa ne kuma biyu Yarabawa ne yayinda suke wajen mai shayi cin Indomie. Maharan basu dauki komai ba, kuma basu amshi abu hannun kowa ba.” “Hari na biyu an kai Igba. An kashe mai suya daya. Saboda haka ba barayi bane, hari aka kawo wa Hausawa a Ondo.” Da farko kakakin yan sanda jihar, SP Funmilayo Odunlami, tace ba hari aka kaiwa Hausawa ba, yan fashi ne.

Kisan ya faru ne a kusa da Sabo da Igba a cikin garin Ondo a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Wata majiya ta ce wasu ’yan kungiyar asiri ne suka kai hari kan wata kungiyar asirin. An tattaro cewa, wani direban kasuwa da ya tsaya cin abinci a yankin an harbe shi shima har lahira.

Ga Bidiyon Ku Kalla Daga Bakin Sarkin Hausawa

https://youtu.be/CbCINvVNrcs

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button