Uncategorized

BIDIYO: Saurayin Jaruma Hadiza Gabon Ya Makata A Gaban Kotu Kan Zargin Yaudara Da Kin Amincewa Ta Aure Shi

BIDIYO: Saurayin Jaruma Hadiza Gabon Ya Makata A Gaban Kotu Kan Zargin Yaudara Da Kin Amincewa Ta Aure Shi.

Wani mutun mai shekaru 48 kuma ma’aikacin gwamnati, Bala Musa ya maka fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon a kotun Shari’ar Musulunci da k jihar Kaduna ta Najeriya saboda ta ki auren sa.

Mai shigar da karar ya shida wa kotun cewa, ya jima yana soyayyaa da jarumar kuma har ta yi masa alkawarin za ta aure shi.

Musa ya shaida wa kotun cewa, kawo yanzu, ya kashe wa jarumar zunzuruntun Naira dubu N396, yana mai cewa, ba ya kyashin ba ta kudi a duk lokacin da ta nema daga gare shi, duba da cewa, yana da kwarin guiwar zai aure ta.

Ya kuma kara da cewa, Gabon ta ki zuwa birnin Gusau da ke jihar Zamfara domin ziyartar sa duk da cewa, ya kintsa tarbar ta.

Tuni dai kotun Shari’ar Musuluncin ta fara zaman sauraren karar a ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito.

Alkalin kotun Malam Rilwanu Kyaudai ya dage zaman shari’ar har zuwa ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa.

https://youtu.be/xV-0xczZfK4

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button