News

BIDIYO: Wallahi Bani Na Kashe Haneefa Abubakar Ba Inji Abdulmalik Tanko Sai Dai Koto Taki Amincewa

Kotu Ta Ki Amincewa Da Matsayar Abdulmalik Da Ya Ce Ba Shi Ya Kashe Hanifa Ba

A ci gaba da sauraron shari’ar Abdulmalik Tanko da wasu mutane biyu wanda ake tuhuma da laifin kashe dalibar makaranta ‘yar shekaru hudu wato, Hanifa, a yau alkalin babbar kotun Kano Mai Sharia Usman Na’abba ya yanke hukunci.

Wannan na zuwa ne biyo bayan bukatar lauyoyin shi Abdulmalik Tanko ta musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Wannan na zuwa ne biyo bayan bukatar lauyoyin shi Abdulmalik Tanko ta musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Hanifa dai daya ce daga cikin daliban makarantar shi Abdulmalik dake Unguwar Dakata a nan birnin Kano.

Sai dai bayan fara gabatar da shaidu a gaban babbar kotun Kano karkashin jagorancin Justice Usman Na’abba.

Ayayin zaman kotun na makon jiya sai kawai Abdulmalik Tanko ya musanta wancan ikirari na sa na fari, yana mai cewa, tilasta masa aka yi ya amsa laifin.

Nan take dai lauyoyinsa suka gabatar da bukata ta musamman, suna masu rokon kotu ta yi nazari akan wannan hanzari na a Abdulmalik Tanko tare da amincewa da abin da ya ambata.

Gadai Bidiyon Ku Kalla

https://youtu.be/bx-1MfeJMXw

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button