Uncategorized

BIDIYO: Wani Matashi Mai Suna Abba Tukur Ya Rubuta Harufan Sunan Atiku Da Zanen Gini

WANI MATASHI MAI SUNA ABBA TUKUR YA RUBUTA HARUFAN SUNAN ATIKU DA ZANE

Wani fasihin matashi mai basirar zane-zanen irin na gidaje da sauransu, mai suna Abba tukur makama Dogondaji, ya rubuta sunan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da zanen fasalin ginin gida.

Matashin wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Tambuwal ne a Jihar Sokoto da ke da mazauni a bayan makarantar koyon aikin jinya, ya yi wannan zane ne saboda soyayyar da ya ke yi wa Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.

Kimanin watanni shida matashin ya kwashe ya na wannan zane wanda kuma duk harafi ɗaya cikin harufan da su ka haɗu su ka ba da sunan Atikun akwai ma’anar da ya ke nufi bisa tsarin zanen da ya yi domin nuna soyayyarsa gare shi.

Wannan ita ce lambar matashin ga waɗanda su ke son sanin ma’anonin harufan a zanen da ya yi ko yaba masa: 08133977317

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button