Uncategorized

DA DUMI-DUMI: Bidiyon Rundunar Tsaron DSS Ta Farin Kaya Tayi Nasarar Damke Kwamandan ISWAP A Kano

DA DUMI-DUMI: Bidiyon Rundunar Tsaron DSS Ta Farin Kaya Tayi Nasarar Damke Kwamandan ISWAP A Kano

Rundunar tsaro ta farin kaya ta DSS a Najeriya ta tabbatar da kama kama wani da take zargin ɗaya ne daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ISWAP a Kano.

Rundunar tsaron ta dai kama wanda ake zargin tare da wasu daga cikin yaransa a daidai lokacin da suke shirya kai wasu hare-hare na ta’addanci a Kano.

Mutumin, wanda jami’an DSS suka kama da ake yi wa laƙabi da Malam Abba, an kama shi ne a unguwar Samegu a yankin karamar hukumar Kumbotso a Kano.

DSS ta ce ta sami nasarar kama Malam Abba da waɗanda aka kama shi da su bayan samun wasu bayanan sirri.

Sannan wanda ake zargin shi ne mai bayar da horo, da shirya hare-haren da ISWAP din za ta kai a jihar.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babban hafsan tsaro Najeriya janar Lucky Irabor ke cewa rudunar tsaron kasar ta daƙile wani yunƙurin kai hari a Kano wanda suka ce zai iya zama “mafi muni” a ƙasar.

Janar Irabor ya ƙara da cewar sun daƙile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari wata coci da ke garin Owo na Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka kashe fiye da mutum 40.

Sannan sun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su, tare da ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasar ciki har da Abuja.

Idan za a iya tunawa a ranar 17 ga watan Mayu aka sami fashewar wata tukunyar gas a titin Aba da ke Sabon gari a Kano, da ya yi sanadiyar mutuwar mutum tara tare da jikkata wasu da dama.

Sai dai an sami rabuwar kai tsakanin al’umma mazauna yankin da jami’an tsaro, inda mazauna yankin ke cewa bom ne, yayin da jami’an tsaro ke cewar tukunyar gas ce da ke waje ta fashe.

Haka zalika kwanaki kadan da faruwar wannan al’amari rudunar ƴan sandan Kano ta ce ta ga wata mota maƙare da kayan hada bom a unguwar Bugaje a yankin karamar hukumar Kumbotso.

Jami’an tsaron sun yi zargin cewar an shiga da motar ne daga jihar Jigawa da ke maƙwabtaka da Kanon.

Tuni dai hukumomi a Najeirya suka tabbatar da ayyukan Mayakan ISWAP a jihar Kaduna da wasu dazuzzuka da ke arewa maso yammacin Najeirya, da ake fama da matsalolin masu garkuwa da mutane.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button