Uncategorized

TASHIN HANKALI: Ku Kalli Yadda Aka Shiga Har Gida Akayi Garkuwa Da Matar Shugaban Jam’iyyar APC Na Karamar Hukumar Magama A Jihar Neja

An Yi Garkuwa Da Matar Shugaban Jam’iyyar APC Na Karamar Hukumar Magama A Jihar Neja

Daga Nuruddeen Isyaku Daza Minna

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matar shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Magama, Alhaji Abubakar Bappa Ibeto, wato Malama Habiba Bappa a gidansa da ke Nateco cikin garin Minna a jihar Neja.

Wani makusancin Bappa, ya bayyana cewar lamarin ya faru ne da asubahin ranar Litinin inda suka shiga har cikin gidansa suka yi awon gaba da matar.

Ya ce, “Zuwa yanzu dai ba mu san halin da take ciki ba, kuma ba wanda ya kira waya don tattaunawa da shi, muna dai rokon Allah ya kubutar da ita cikin qoshin lafiya.”

“Lokacin da abin ya faru shi Bappa baya gari domin ya yi tafiya, amma mun gaggauta sanar da jami’an tsaro kan faruwar lamarin.”

Ko a kwanakin baya dai, wasu fusatattun matasa, sun farmaki tawagar Bappan a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Neja, inda ya tsallake rijiya da baya, bayan sun faffasa gilasan wasu motocin da ke cikin tawagar.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tana binciken faruwar lamarin tare da alkawalin kubutar da ita cikin koshin lafiya

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button