News

BIDIYO: Wasu rubabbun kudade da aka gano cikin Buhuhuna sun ja hankalin ‘yan Najeriya

BIDIYO: Wasu rubabbun kudade da aka gano cikin Buhuhuna sun ja hankalin ‘yan Najeriya

Subahanallahi! Kalli bidiyon Wasu rubabbun kudade da aka gano cikin Buhuhuna sun lalace wanda ya ja hankalin ‘yan Najeriya.

Rahotanni sun ce an gano buhunan rubabbun takardun kudi na naira a barikin ‘yan sanda a Jihar Benue.

Wani faifan bidiyo da aka yada a yanar gizo ya nuna buhunan kudi na miliyoyin Naira da suka lalace da aka ce an gano su a barikin ‘yan sanda na Wadata dake jihar Benue.

Ana iya jin wata muryar mutane a cikin faifan bidiyon suna cewa, “Kalli kudi a Wadace amma sun rube, duba kudi, duba inda aka boye kudi har aka bari suka lalace.

Wannan bidiyo Ba karamin daukar hankalin mutane yai ba, musamman ma talakawa inda sukai tofa Albarkacin bakinsu.

A gefe Guda kuma malamai na kira da Al’ummar kasa da suyi karatun ta nutsu wajen zabar Shuwagabannin da suka cancanta a kasa.

Saboda kaucewa fadawa cikin irin wannan yanayi dakoma cikin kangin talauci da fatara a kasa

https://youtu.be/hcL2Thrmros

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button