News

Wata kotu A Kano Ta Yanke Wa Dan Hisbah Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Wata kotu A Kano Ta Yanke Wa Dan Hisbah Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Daga Sani Musa Mairiga

Wata babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 9 ta yankewa wani tsohon dan Hisba, mai suna Dayyabu Muhammad, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu, ta samu tsohon ma’aikacin Hisbar ne da laifin kisan wata bazawararsa mai suna Hauwa Ibrahim, laifin da ta ce ya saba wa sashe na 221 na Kundin Penal Code.

Wata majiya ta shedawa wakilin mu cewa, Dayyabu tsohon ma’aikacin Hisba ne kuma ya kasance almajirin gidan su Hauwa, inda ya nuna ra’ayinsa na aurenta, har suka fara soyayya.

Daga bisani Dayyabu ya yi maganar auren, amma iyayenta suka ce ba su yarda da tarbiyyarsa ba, don haka ba za su ba shi ’yarsu ba.

Daga bisani ita ma Hauwar ta nuna ba ta ra’ayinsa.

Hakan ne ya fusata Dayyabu inda ya je har gida a shekarar 2011 ya samu marigayiyar tana kwance a daki ya ce ya zo ne su yi sallama.

Nan take ya dauko wuka ya fara caccaka mata a ko ina na jikinta, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button