News

BIDIYO: Yadda Aka Biya Kudin Fansar Sa Da Katon 6 Na Giya Da Babura 2 Da Kudi Nara 500.000

Ƴan ta’adda sun saki wani mutum da su ka yi garkuwa da shi bayan an basu giya katan 6, babura 2 da N500,000

Ƴan ta’adda sun saki wani mutum ɗan Jihar Kano mai suna Muktari Ibrahim bayan da iyalin sa su ka cika sharuɗɗan sakin nasa masu tsauri da aka gindaya musu.

Tun a ranar 21 ga Nuwamba, 2021 a ka ɗauke Ibrahim tare da wasu matafiya a kan titin Abuja-Kaduna.

Sai a ranar Laraba ya shaƙi iskar ƴanci bayan ya shafe kusan watanni uku a hannun masu garkuwa da mutane.

Daily Nigerian ta jiyo cewa tun sanda a ka yi garkuwa da Ibrahim iyalin sa su ke ta fafutukar biyan kuɗin fansar sa, bayan da ƴan ta’addan su ka nemi a biya su Naira miliyan 50 har da ga bisani a ka dawo N500,000, katan ɗin giya 6 ta kamfanin Lager da kuma babur Bajaj guda 2.

Wata majiya da ga iyalin mutumin ta ce tun da fari dai ƴan ta’addan sun matsa sai dai a basu babur samfurin Boxer, amma da su ka tuna musu cewa an hana sayar da Boxer ɗin a jihohi da dama, sai su ka yarda a basu Bajaj ɗin.

Daga nan, in ji majiyar, sai su ka sake shi ba tare da sun bashi ko kuɗin mota ba, inda su ka ce masa idan ya fita ya roƙi masu unguwanni a kan hanya su nuna masa hanya daga jejin.

Bayan ya fito sai ya haɗu da wani mai gari, inda ya tausaya masa ya bashi N300 da ga nan ne ya hau mota zuwa Zariya.

https://youtu.be/3GB48PzCLQA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button